Da yiwuwar gwamnonin PDP Tinubu su ke yi wa aiki, in ji Dele Momodu

Da yiwuwar gwamnonin PDP Tinubu su ke yi wa aiki, in ji Dele Momodu

Jigo a jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya zargi wasu gwamnoni da aka zaba a karkashin jam’iyyar da yin aiki a asirance ga Shugaba Bola Tinubu, musamman ma wadanda ke adawa da hadewar jam’iyyun adawa.

Jaridar DAILY NIGERIA ta ruwaito cewa gwamnonin PDP, bayan wani taro da suka gudanar a birnin Ibadan ranar Litinin, sun bayyana cewa ba za su yi wani hadin gwiwa ko hadewa da wata jam’iyya ba kafin zaben shekarar 2027.

Amma a wata hira da aka yi da shi a tashar Arise  a ranar Litinin, Dele Momodu ya ce babu wata jam’iyyar adawa daga cikin manyan jam’iyyun da za ta iya kada Tinubu daga mulki ita kadai a 2027.

Mawallafin mujallar Ovation ya shawarci jam’iyyun adawa da su hada kai kuma su yi amfani da dabarun da jam’iyyar APC ta yi amfani da su a 2015 wajen lashe zabe.

“Shugabannin jam’iyyun adawa sun kuduri aniyar yin aiki tare a wannan karon. Gaskiyar magana ita ce, Atiku ba zai iya shi kadai ba, Peter Obi ba zai iya shi kadai ba, haka nan Rabiu Kwankwaso ma ba zai iya shi kadai ba.

“Saboda haka dole ne su samo hanyar da za su rama wa APC da irin abin da ta yi, ta hanyar hada wani kaso daga cikin jam’iyyun – har da APC kanta – domin su yi aiki tare.

“Idan gwamnoninmu suna cewa a’a, ba za mu shiga wani hadin gwiwa ba, to hakan yana nufin a boye suna aiki ne don gwamnatin Tinubu".