Sabbin dokokin haraji za su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026 — Fadar Shugaban Ƙasa

Sabbin dokokin haraji za su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026 — Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa sabbin dokokin haraji a Nijeriya za su fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026, kamar yadda aka tsara tun da farko, tare da yin watsi da kiraye-kirayen dakatar da tsarin gyaran harajin.

A cikin wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa da aka fitar a ranar Talata, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gyare-gyaren harajin, ciki har da waɗanda suka fara aiki a ranar 26 ga Yuni, 2025, da kuma sauran da aka tsara su fara aiki a 2026, za a aiwatar da su kamar yadda aka tsara.

Shugaban ƙasar ya bayyana gyaran harajin a matsayin wata dama ta musamman “sau ɗaya a cikin ƙarni” don gina tsari mai adalci da ɗorewar tsarin kuɗaɗen gwamnati ga ƙasar.

Ya jaddada cewa sabbin dokokin harajin ba an tsara su ne domin ƙara nauyin haraji ba, sai dai domin aiwatar da gyaran tsari, daidaita tsarin haraji, da kuma ƙarfafa alƙawarin zamantakewa tsakanin gwamnati da jama’a tare da kare martabar ’yan ƙasa.

Tinubu ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ba da goyon baya ga matakin aiwatarwa, inda ya ce gyaran harajin yanzu ya shiga cikakken matakin aiwatar da shi.

Da yake magana kan muhawarar da ake yi a bainar jama’a game da zargin sauye-sauye a wasu sashe na dokokin harajin da aka riga aka kafa, Shugaban ƙasar ya ce babu wani muhimmin lamari da aka gano da zai sa a dakatar ko a kawo cikas ga tsarin gyaran harajin.

Ya ƙara da cewa amincewa da gwamnati ana gina ta ne a hankali ta hanyar yanke shawarwari masu kyau, ba ta hanyar ɗaukar matakan gaggawa marasa nazari ba.

Shugaban ƙasar ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na bin ka’idojin doka da mutunta dokokin da aka riga aka kafa, inda ya yi alkawarin cewa fadar shugaban ƙasa za ta yi aiki tare da majalisar dokoki ta ƙasa domin warware duk wata matsala da ka iya tasowa cikin gaggawa.