Shugaban riko na APC a Zamfara,  ya caccaki Yariman Bakura  kan kalaman sa na rijistar APC

Shugaban riko na APC a Zamfara,  ya caccaki Yariman Bakura  kan kalaman sa na rijistar APC
Shugaban riko na APC a Zamfara,  ya caccaki Yariman Bakura  kan kalaman sa na rijistar APC
 
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
 
 Shugaban, Kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara, Alhaji  Lawal M. Liman ya caccaki tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura kan kalaman da ya fada wadanda suka kawo takaddama   game da aikin sake rijistar  membobin Jam’iyyarsu  a Jihar.
 
 Liman ya ce, Yarima ba shi da ikon soke rajistar da 'ya'yan jam'iyar APC suka yi tun kafin shigar Gwamna Matawalle a jam'iyya, ya kara da  cewa ya kamata a yi watsi da maganarsa domin na yaudara ne.
 
 Ya kara da bayyana cewa Yarima dan siyasa ne mai son shi kadai ke gudanar dar harkokin jam'iyya a wannnan jihar,  wanda ya rasa daukaka saboda halinsa na dan siyasa mai fuska biyu.
 
 Shugaban ya yi bayanin cewa, Jam'iyyar APC a  Zamfara ta riga ta yi rijistar mambobi sama da 770,000 kuma dukkan gundumomi 147 na jihar ne ke kula da rijistar kamar yadda sashe na  9 (8) na tsarin mulkin APC ya tanada.
 
 Lawal Liman ya yi gargadin cewa, ta hanyar amfani da  9 (5) na kundin tsarin mulkin APC ba za a iya dakatar da rijistar membobi ba sai in mutun ya rasu, ko an kore shi daga jam'iyya ko yayi  murabus don  karbar mukami daga 'yan adawa, sai kuma  canja shekar  memba daga wata Jam'iyyar siyasa, zuwa wata.
 
 Ya ci gaba da cewa, kalaman shedana  da yaudara da Yariman Bakura ya yi, cewa an soke rajistar memba sama da 770,000 ba shi da tushe kuma yunkuri ne na tarwatsawa da kuma raba   kawunan 'yan siyasa  da yi wa jam’iyya zagon kasa da kuma  yaudarar jama’a.
 
 Shugaban riko na APC ya lura da cewa, gwamnoni da yawa sun koma jam'iyyar  APC, na baya -bayan nan su ne na jihar Ibonyi da na Cross River gwamnonin da za su canza sheka zuwa APC amma ba a soke rajistar membobinsu na jiha ba, me ya sa sai  Zamfara?  Liman ya tambaya.
 
 Don haka ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su watsar da sanarwar Yarima kuma su ci gaba da rijistar membobinsu saboda yana da inganci kuma babu wanda zai iya soke wannan rijistar da suka yi.