Fargaba a Sakkwato Yayinda Kotun Koli Za Ta Soma Sauraren Karar Mainasara Da APC

Fargaba a Sakkwato Yayinda Kotun Koli Za Ta Soma Sauraren Karar Mainasara Da APC

Kotun kolin Nijeriya ta Sanya gobe Talata ne za ta soma sauraren Karar da ke gabanta wadda Honarabul Mainasara Sani ke kalubalantar sahihancin zaman Isah Sadik Achida shugaban jam'iyar APC a Sakkwato.
Karar wadda aka Sanya a cikin wannan wata na Oktoba amma ba a soma ba domin kotun kolin ta nemi da Mai Karar ya gyara Shari'ar ganin yanda ya fita batun maganar kafin ya waiwayi lamarin daga baya.
Mai Karar ya bi umarnin kotun hakan ya sa ya sake tunkarar kotun Koli da maganar in da yake son ta tabbatar masa da shi ne shugaban jam'iyar APC a Sakkwato Wanda aka zaba a zaben shugabannin jam'iya da aka yi a shekarar data gabata.
In har kudirin nasa ya tabbata kotu ta ba shi nasara ana ganin hakan zai iya mayarda hannun agogo baya a jam'iyar APC.
Managarciya ta fahimci Fargaba ta mamaye magoya bayan jam'iyar APC a Sakkwato ganin harkar shari'a abu ne da ba a San mi zai faru ba har sai an kammala.
Hankalin 'yan siyasa ya koma kan lamarin Shari'ar sun zuba Ido su ga yanda za ta kaya a kotun kolin.