Kakakin Majalisar Dokokin Sakkwato Ya Fice Daga APC Zuwa PDP

Kakakin Majalisar Dokokin Sakkwato Ya Fice Daga APC Zuwa PDP

Shugaban majalisar dokokin jihar Sakkwato Honarabul Aminu Muhammad Achida ya bar jam'iyar APC ya koma jam'iyar PDP.
Kakakin ya gabatar da takarda a zaman majalisa da ya gudana Alhamis don sanar da ficewarsa.
Haka ma ɗan majalisa mai waƙiltar ƙaramar hukumar Wamakko Murtala Bello Maigona shima ya bar APC zuwa PDP.
Mutanen sun daɗe suna rigima da jam'iyar APC tun bayan shigarsu a majalisa a 2019 sanda suka yi gaban kansu a wurin saɓawa tsarin jagororin APC a Sakkwato.
Mafi rinjayen magoya bayan APC sun yi tsammanin za su bar jam'iyar ganin yanda suka ƙauracewa dukkan taronta na masu ruwa da tsaki.