Zulum ya ba da  umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin ba

Zulum ya ba da  umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin ba
 Zulum ya ba da  umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin ba

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara  Zulum, ya umarci jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da su kamo duk wani malamin da ke wa’azi a fili tare da tunzura jama’a da gwamnati ba ta san da shi ba. 

Gwamnan, ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da masu ruwa da tsaki a taron tattaunawa kan yanayin tsaro na jihar wanda ya samo asali daga mika wuya na daruruwan mayakan Boko Haram a gidan gwamnati ranar Lahadi a Maiduguri.
Gwamnati ta fahimci malaman da ke wa'azi ba tare da izinin gwamnati ba suna tunzura jama'a tare da kawo cikas ga harkar tsaron jiha.

Da yawan mutane na ganin rashin sanya doka ne kan malamai ke sa suna yin gaban kansu wurin kawo fahimta mai rikitarwa a cikin al'umma wadda a ƙarshe ke zama alƙaƙai a cikin jama'a.