PDP Ta Ɗunke Ɓarakar Da Ke Cikinta A Jihar Sakkwato

PDP Ta Ɗunke Ɓarakar Da Ke Cikinta A Jihar Sakkwato

Jam'iyar PDP a jihar Sakkwato ta ɗunke ɓarakar da take fama da ita tun bayan kammala zaɓen tsayar dan takarar gwamnan jiha a 2023.
PDP ta shirya taron kaddamar da kwamitin kamfe a ɗakin taro na ƙasa dake Ƙasarawa in da dukkan 'yan takarar da suka nemi jam'iyar ta ba su damar tsayawa takarar gwamna  suka halarta.

Halartar mataimakin gwamnan jiha Manir Muhammad Dan'iya da tsohon mataimakin gwamna Barista Mukhtar Shehu Shagari hakan ke nuna jam'iyar ta shawo kan matsalarta da alamu kuma ta ɗinke lamarin.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a wurin taron ya sanar da janyewa kan mukaminsa na shugaban kwamitin yakin zaɓe kuma tsohon gwamna Attahiru Bafarawa ne zai maye gurbinsa domin yanayin aikinsa na ƙasa a jam'iyar PDP.

Tambuwal ya kuma sanar da jama'a su sani bai yi alƙawali da ɗan takarar Gwamnansa in ya samu nasara ya riƙa ba shi wasu kuɗi duk wata, da bashi wasu kujerun muƙami ya baiwa wasu na tare da shi ba. Abin da wasu ke kallon shaguɓe ne ya yi ga wamda ya gada.
Ya ce abin da kawai yake so ya yiwa mutane aiki a jiha.