Kotu ta dakatar da shugaban PDP na ƙasa 

Kotu ta dakatar da shugaban PDP na ƙasa 
Kotu ta dakatar da shugaban PDP na ƙasa 

Babbar kotun jihar Rivers da ta yi zamanta a garin Fatakwot ta amince da buƙatar da aka sanya a gabanta na neman hana shugaban jam'iyar PDP Uche Secondus ya ci gaba da kiran kansa shugaban PDP.

Amincewar ta zo ne kan shari'ar da wasu mambobin jam'iyar Ibeawuchi Ernest Alex, Dennis Nna Amadi, Emmanuel Stephen da Umezirike Onucha suka shigar gaban kotu na ƙalubalantar Secondus.

Alƙali  O. Gbasah ya ba da umurnin ne a ranar Litinin cewa Secondus ya daina kiransa mamba a jam'iyar PDP.

Alƙalin ya dakatar da Secondus ya jagoranci kowane taro ko kwamitin jam'iyya a matakin mazaɓa ƙaramar hukuma da jiha.