PDP Na Shirin Naɗa Tambuwal Darakta Janar A Yakin Zaɓen Atiku A 2023
Wata majiya a jam'iyar PDP ta sanar da jaridar The Nation akwai wata sabuwar fargaba a cikin jam'iyar in da wasu jagorori ke shirin ganin gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya zama Darakta Janar a yakin zaben shugaban kasa na Atiku Abubakar a zaben 2023.
Tambuwal ya janyewa Atiku takararsa a lokacin zaben fitar da gwani na jam'iyar kuma a yanzu yana neman kujerar shugaban majalisar dattijai matukar shi da Atikun suka lashe zaben kujerunsu a shekara mai zuwa.
Majiyar ta ce baiwa Tambuwal Darakta Janar zai kara sanya mutanen Kudu yin korafi da mita ganin PDP ta koma ta Arewa ganin yanda shugaban jam'iya da shugaban kwamitin amintattu da dan takarar shugaban kasa da mai magana da yawun ɗan takarar duka daga Arewa suke, yin haka ba adalci ba ne ga PDP.
Wasu shugabanni suna ganin abaiwa gwamnan Oyo Seyi Makinde muƙamin duk da wasu na ganin haɗa mashi wannan aiki da nasa na neman sake zama Gwamna a karo na biyu nauyin ya yi masa yawa.
Wasu jagororin PDP na ganin miƙa matsayin ga mutanen Wike shi ne ya fi da cewa ga PDP.
managarciya