Atiku da Tambuwal sun ziyarci Obasanjo an yi ganawar sirri ta awa biyu

Atiku da Tambuwal sun ziyarci Obasanjo an yi ganawar sirri ta awa biyu

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyara don ganawa da tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, Jihar Ogun.

Ayarin motocin Atiku sun isa Dakin Karatu na tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (OOPL), Abeokuta, da misalin karfe 12:36 na rana, in da suka shafe awa biyu suna ganawa ta sirri.

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya samu tarba daga abokin Obasanjo, Otunba Oyewole Fasawe.

A cikin ayarin Atiku akwai tsoffin gwamnonin jihohin Cross River da Sokoto, Liyel Imoke, Sanata Aminu Tambuwal, da Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Atiku ya shiga kai tsaye zuwa ganawar sirri tare da tsohon shugaban nasa.