Tsaro a Katsina: Ka gaya ma Buhari kawai ya gaza - PDP ta gayawa Masari

Tsaro a Katsina: Ka gaya ma Buhari kawai ya gaza - PDP ta gayawa Masari
Tsaro a Katsina: Ka gaya ma Buhari kawai ya gaza - PDP ta gayawa Masari
 
Jam'iyyar PDP mai adawa a Nijeriya, ta mayar wa Masari martani game da maganar da ya yi na cewa, wasu kananan hukumomi guda goma a jihar Katsina na fama da yawaitar kai hare-haren 'yan bindiga masu tayar da kayar bai.
 
PDPn ta ce Masari ya daina wata kwana-kwana ya fito karara kawai ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari da jam'iyyar APC sun gaza samar da tsaro kamar yadda suka alkawuranta tun a baya.
 
A jawabin da Kakakin PDPn ya fitar Kola Ologbondiyan, da Katsina Daily Post News ta gani, jam'iyyar ta PDPn ta ce abin kunya ne a ce jihar shugaban kasa, tsaro ya gagara, kullum sai an kashe mutane, ko an sace su kwanciyar hankali ya gagara samuwa.
 
PDPn ta bayyana cewa ba dacewa ba ne, a ce shugaban kasa na can na ta wasu maganganun da ba su dace ba a Abuja, amma jiharsa kamar yadda Gwamna Masari ya ambata kananan hukumomi goma na fama da yawaitar hare-haren 'yan bindiga a kullum, a don haka jam'iyyar ta kira Buhari a matsayin wanda ya gaza a bisa muhiman kudurorinsa da suka hada da tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da rashawa ba wai a tsaya ana wasu kame-kame ba.