Daga Babangida Bisallah, Minna
A daidai lokacin da ake tunkarar babban zaben 2023, jam'iyyar APC tana kokarin kafa shugabancin jam'iyya daga matakin mazabu zuwa kananan hukumomi kamar yadda uwar jam'iyya ta kasa ta ba da umurni.
Sai dai a lokacin da wasu jahohi ke gudanar da na su zaben shugabanni ko nadi, jihar Naija ta shiga cikin wasu jahohin da nadi ko zaben ya fuskanci kalubalen rashin amincewar wasu 'yayan jam'iyyar.
Binciken da jaridar Managarciya ta gudanar, ta fahimci cewar tsoffin yayan jam'iyyar da suka faro tafiyar tun daga tsohuwar jam'iyyar CPC da suka yi hadin guiwa da ta zama APC a yau suna zargin daga cikin wadanda aka damkawa amanar kafa shugabancin jam'iyyar na yunkurin kashe tasirin yayan jam'iyyar na asali inda suke yunkurin kafa shugabancin jeka na yi ka dan su samu damar murza gwamnatin da suke tsammanin kafawa a gaba.
Tun dai fara kafa shugabancin jam'iyyar a matakin mazabu zuwa jiha jam'iyyar ke fuskantar matsalolin cikin gida da yanzu haka ya kai ga kafa shugabancin jam'iyyar a matakin jiha zuwa gida biyu.
Da yake amsa tambayar manema labarai, tsohon kwamishinan makarantun kimiyya ta jiha, Hon. Abubakar Katcha, yace ba muna rigima da gwamnati ba ne, ba kuma muna son kawo hatsaniya ba ne, illa muna kokarin ganin an yi adalci ne wa yayan jam'iyya.
Da farko an shelanta sayar da fom ga yan takarar mukamai a cikin jam'iyya, bayan sun saye fom sun biya kudaden su kamar yadda jam'iyya ta tsara, sai a ka bullo mana a rana tsaka cewar ba za a gudanar da zaben ba, za a yi sulhu ne tsakanin yan takara.
Sai muka fahimci cewar akwai wadanda ke muradin kafa wadanda suke so ne kawai ba tare da amincewar jama'a ba, domin ba dan takarar da yan kwamitin da aka ce an kafa suka kira, kuma su wadanda suka sayi fom ba wanda aka dawo wa da kudinsa, sannan inda suka sayi fom din aka tura jami'an tsaro aka hana su duba sunayen su kamar yadda dokar ta tsara.
Ganin hakan ya sa tunda mu halastattun yayan jam'iyya ne kuma mu ne kwamitin samarwa jam'iyyar cigaba da samun kudaden shiga mu ka ki amincewa da tsarin su, mun rubuta takardar koke ga uwar jam'iyya, dan sanar ma ta halin da mu ke ciki a Naija.
Yanzu haka mun kammala zaben sabon shugaban jam'iyya ta jiha, inda Hon. Nasiru Yusuf Ubandiya ya samu nasara da kuri'a 1469, yanzu mun umurci yayan jam'iyya da suka sayi fom ba a ba su damar yin takarar ba da su tattara rasitai da takardun shaida dan mikawa uwar jam'iyya ta kasa da sakamakon zaben da mu APC original muka gudanar, sannan za mu tabbatar mun mikawa kotu korafe-korafen su dan bin kadin hakkin su.
A dai safiyar asabar din makon da ya gabata da APC Original kamar yadda suke ikirari suka gudanar da zabe tare da rantsar da shugaban jam'iyya a bangaren su suka gudanar, yan awowi kuma bangaren gwamnatin jiha ta gudanar da na ta zaben, inda aka zabi Hon. Haliru Jikantoro a matsayin sabon shugaban jam'iyya ta jiha.
A bayanin sa, ya godewa yayan jam'iyya bisa goyon bayar da suka bayar na zabensa, sannan ya yabawa kwamitin riko na jam'iyyar ta jiha suka taka na hada kan yayan jam'iyyar waje daya da har aka cin ma nasarar wannan zaben ba tare da hargitsi ba.
Jikantoro ya bayyana cewar ya yafewa dukkan wadanda suka samu rashin fahimta na siyasa, kofarsa a bude take dan yin tafiya da kowa ba tare da nuna bambanci ba.
Yayi fatar wadanda suka samu nasarar wannan zaben da zasu yi aiki tare da shi, da su hada karfi da karfe dan yiwa jam'iyyar APC hidima kamar yadda suka alqarwanta.
Yanzu dai yayan jam'iyyar da jama'ar jihar sun sanya ido ganin yadda za ta kaya ga jam'iyyar musamman ganin yadda zaben fitar da gwani na yan takarar kujerun siyasar 2023 za ta kaya musamman ganin yadda babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke kokarin ganin ta dunke matsalolin ta na cikin gida, a lokacin jam'iyyar APC mai mulki ke darewa. Ganin taken jam'iyyar shi ne tsintsiya madaurin ki daya, shin kafin 2023 tsintsiyar za ta kasance haka ko za ta watse.i