2023: Dan Majalisar Dokoki a Sakkwato  Ya Sha Kaye a Kotun Daukaka Kara

2023: Dan Majalisar Dokoki a Sakkwato  Ya Sha Kaye a Kotun Daukaka Kara

 

Dan majalisar dokokin jihar Sakkwato Alhaji Aminu Bodai ya sha kaye a kotun daukaka kara dake zamanta a Sakkwato kan shari'ar da ya sa a gabanta in da ya hakikance shi ne dan takarar dan majalisar dokoki a APC da zai wakilci karamar hukumar Dange Shuni a zaben 2023.

Mai Shari'a M L Shu'aibu a madadin sauran alkalan ya kori shari'ar Aminu Bodai tare da tabbatarwa Sirajo Muhammad takararsa ta dan majalisa a inuwar jam'iyar APC kan gamsuwa da hujjar bai janye takararsa ba bayan samun nasara a zaben fidda gwani da jam'iyarsu ta gudanar.
Alkalin ya tabbatar hujjojin da aka gabatar na janyewar ba su tabbata ba.
 Sirajo Shuni bayan kammala zaman kotun ya zanta da wakilinmu in da yake cewa ya gode Allah, yana kira ga 'yan jam'iya da magoya bayansa su zauna lafiya domin harka ce ta jam'iya abu guda suke lamari ne na cikin gida, kar a ci zarafin kowa, suna yi ne don neman hakkin wadan da suka wakilta su don tsayawa takara.
"ina da kwarin guiwa samun nasarar lashe zabe a 2023, ganin yanda kotu ta yi tsaye kan gaskiya da adalci abin yabawa ne, musamman lauya na da ya yi aiki ba tare dana biya shi ba," a cewarsa.
Ka shirya zuwa kotun koli in wanda ke jayayya bai gamsu da wannan hukuncin ba? ya ce "in sha Allah ma ba zai je ba, domin yana yin abubuwansa saboda mutane, an ce ya je ya yi biyayya ga magoya baya, na yi nasara a kotun farko da ta biyu, nasan zai bari domin hukunci ne daga Allah, in kuma ya tafi zan sake samun nasara da ikon Allah,"in ji Sirajo Shuni.
Ya ce yafi sauran 'yan takara cancanta dake wasu jam'iyyu da yawan mutanen da ba su APC za su zabe shi domin samar da cigaba a yankinsu.