NNPP ta ƙalubalanci Ganduje kan ɗaukar ma'aikata da tallafin karatu a Kano

NNPP ta ƙalubalanci Ganduje kan ɗaukar ma'aikata da tallafin karatu a Kano

Jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar Kano ta zargi gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da durkusar da ma’aikatun gwamnati a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na jihar Umar Haruna Doguwa da ya raba wa manema labarai a jiya Asabar a Kano.

Doguwa ya yi zargin cewa, ikirarin da gwamnatin jihar Kano ta yi a baya-bayan nan na cewa ta buɗe shafin ɗaukar ma’aikata ta yanar gizo a matsayin farfaganda, da nufin samun bayanan katin zaɓen al’umma, musamman na matasan Kano wadanda ke fama da bukatar aikin yi.

 “Ina son in kalubalanci gwamnatin jihar a yau, idan da gaske suke yi, zasu dauki ma’aikata ofishin shugaban ma’aikata ne ba wai kwamitin ba, ikirarin da ake yi na daukar ma’aikata a halin yanzu yana da shakku. Mun yi imanin gwamnati na son ta samu wasu muhimman bayanai ne a kan PVCs na masu neman shiga”

A cewarsa, “Gwamnatin Ganduje ta yi ƙaurin suna wajen cin hanci da rashawa, rashin ɗa’a, rashin biyan kudin fansho da giratuti, da tsaikon biyan albashi da kuma ci gaba da rage yawan albashin ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a duk wata.

"Amma gwamnati ta ɗauki malamai shekara da shekaru kuma har yanzu sau ɗaya ta biya ɗalibai tallafin karatu tun lokacin da aka fara a 2015. Kuma shi ma biyan kuɗin an yi shi ne kawai a jajibirin babban zaɓen 2019 da nufin zaburar da masu zabe,” ya yi zargi.

Jam’iyyar NNPP ta kuma yi zargin cewa tun tuni gwamnatin ta janye daga aiwatar da biyan mafi karancin albashi na dubu talatin (N30,000) wanda doka ta amince da shi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Ganduje ma ta amince da shi tare da yin alkawuran ƙarin da ta yi wa ma’aikatan, "amma har yanzu ba a cika alkawarin ba, kuma a ce wai za’a dauki sabbin ma’aikata?",  a cewar Doguwa

"Ya dace a sanar da al’ummar Kano cewa dubban ma’aikatan gwamnatin da ake da su ko dai sun yi ritaya ko kuma sun mutu a hidima a cikin shekaru bakwai da watanni uku na gwamnatin Ganduje da ya kamata a maye gurbinsu da wasu cikin gaggawa domin tafiyar da harkokin gwamnati a jihar.

“Muna kara ja kunnen masu ruwa da tsaki da su ka haɗa da jami’an zaɓe cewa, jam’iyyar NNPP a matsayinta ta babbar jam’iyyar adawa a jihar, ba za ta lamunci maguɗin zabe ba ta kowacce fuska a babban zaɓen 2023, wanda mu ke zargin ana daukar ma’aikatan ne don ayi amfani da su wajen maguɗin zabe, ” in ji Doguwa.