Gwamnatin tarayya za ta gina sabon bye-pass a Kano
Majalisar zartarwa ta ƙasa ta amince da bada kwangilar ginin sabon titi da zai kewaye arewacin Kano (Northern bye pass).
Akwai kuma ƙarin wasu ayyukan da majalisar ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Tinubu ta amince a aiwatar a jihohin Kebbi da Kwara da Kogi da kuma Abuja.
Sabon bye-pass ɗin na Kano wanda zai ratsa daga garin Dawanau ya ɓullo har zuwa Yankaba yana da tsahon kilometre 37 kuma babban kamfanin nan na CCECC ne zai gudanar da aikin.
Aikin zai lashe kuɗi har naira biliyan N230 billion kuma ana sa ran kammala shi cikin watanni 36.
A dai zaman nata na wannan sati majalisar ta amince da farfaɗo da aikin vabbar hanyar d ata tashi daga Sakkwato ta kai har Badagary a jihar Legas. Hanyar, wadda aka ƙirƙiri yinta tun a shekarar 1976 an yi watsi da aiwatar da ita tun bayan lokacin.
Haka nan kuma zaman majalisar ya amince gina hanyar da ta tashi daga Ngaski zuwa Wara a jihar Kebbi, da tsohuwar hanyar Abaji zuwa Koton Karfe da ta haɗa jihar Kogi da Abuja, da hanyar Kaima zuwa Teisse a jihar Kwara.
managarciya