Tsadar Rayuwa:Kasa da Kashi 50 Ne Suka Biya Kudin Aikin Hajji a Nijeriya

Tsadar Rayuwa:Kasa da Kashi 50 Ne Suka Biya Kudin Aikin Hajji a Nijeriya

 Da wuyar gaske Nijeriya za ta mamaye kujerun aikin Hajjin bana a aka ware mata guda dubu 95 domin da yawan maniyatan ba su biya ba, wasu Kuma ba su cika kudinsu ba.
Matsalar harkar canjin kudi ne ta dabaibayi aikin in da kudin kujera yakai 4.9 Miliyan.
Hukumar aikin Hajji ta kasa ta ware kujera dubu 75 a jihohi 36, Abuja dubu 20 ne aka ba su.
Hukumar ba ta fadi yawan wadan da suka biya ba Amma a binciken daily trust ta gano da yawan jihohi ba su saida rabin kujerun nasu ba.