Kashe DPO A Katsina:Sojoji Sun Halaka Yaron Bello Turji Da Wasu 41

Kashe DPO A Katsina:Sojoji Sun Halaka Yaron Bello Turji Da Wasu 41
 

Luguden wuta da Rundunar Sojojin Saman Najeriya, NAF ta yi ta jiragen sama ya hallaka Dogo Umaru, wani ƙasurgumin dan ta’adda, wanda ya ke ƙarƙashin ikon fitinannen shugaban 'yan fashin dajin nan, Bello Turji.

 

Harin bamabamanta na sama  ya kashe wasu 'yan bindiga aƙalla 40.

 
PRNigeria ta jiyo cewa rundunar sojin ta ba da izinin kai harin ta sama bayan an tabbatar da cewa Dogo Umaru da tawagarsa ne su ka shirya wasu hare-hare da aka kai a ƙauyen Magama da ke Ƙaramar Hukumar Jibia a Jihar Katsina.
 
Ɗaya da ga cikin harin da su ka kai a baya-bayan nan ne ya yi sanadiyar rasuwar Babban Jami’in 'yan Sanda na Caji-ofis ɗin  Magama, DPO, yayin da wani soja kuma ya samu rauni a harin.
 
Tuni a ka san cewa Umaru da mayaƙansa ne su ka kai hare-hare a ƙauyukan da su ka kewaye yankin, inda su ke kai harin da ga wata makarantar Firamare ta Tsamben Dantambara, wadda tu daɗe babu kowa a cikin ta.
 
Sai dai PRNigeria ta samu labari daga wani jami’in leken asiri na soji cewa an tura jiragen sama guda biyu domin ‘kashe 'yan ta’addan da ke addabar Katsina.
 
"Daya daga cikin jirgin ya samu nasarar luguden wutar ne a kan gungun 'yan ta'addan, yayin da na biyun kuma ya yi nasarar ya ci keren 'yan ta'addan da su ka tsere," in ji shi.
 
Majiyoyi a yankin da ke kusa da kauyen Tsamben Babare sun tabbatar da cewa, an hallaka ‘yan ta’adda 42 a harin da sojojin saman NAF suka kai musu, inda su ka ce ciki har da Dogo Umaru.
 
Wani jami’in leken asiri na rundunar sojin Najeriya ya ce dakarun soji da na sauran jami’an tsaro sun kara kaimi a rundunoni daban-daban a yankin Arewa-maso Yamma, a kwanan nan.
 
"A makon da ya gabata, wani harin da jirgin NAF ya kai tare da yakin da sojojin kasa suka yi a jihohin Kaduna da Neja sun kawar da 'yan ta'adda da dama a kusa da makarantar horas da sojoji ta Najeriya da kuma wajen Shadadi-Maundu."