Malamai da 'ya'yansu da aka Sace a Jami'ar Abuja Sun Shaki Iskan 'Yanci
Malamai da 'ya'yansu da aka Sace a Jami'ar Abuja Sun Shaki Iskan 'Yanci
Wata sanarwa da Jami'ar Abuja ta fitar ranar Juma'a ta tabbatar da sako ma'aikatan nata da aka yi garkuwa da su ranar Talata.
Sanarwar, da shugaban jami'ar ya fitar, ta ce haɗin gwuiwar jami'an tsaron Najeriya da ta hada da sojoji da 'yan sanda da jami'an DSS ne suka ceto duka mutanen.
A ranar Talata ne 'yan bindigar suka kutsa kai rukunin gidajen Jami'ar da ke Gwagwalada da misalin karfe daya na dare suka malamai guda uku da 'ya'yansu biyu da kuma wani ma'aikacin Jami'ar.
Matsalar satar mutane ta zama ruwan dare a arewacin Nijeriya duk ikirarin da hukumomin tsaro ke yi na dakile lamarin amma 'yan bindigar na cin karensu ba babbaka.
managarciya