Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun jefar da jaririya sabuwar haihuwa a cikin Sikandaren gwamnati da ake kira A.B.A a unguwar Rugar Wauru a birnin Sakkwato.
A ranar lahadin da ta gabata ne wasu yara kanana suka ga jaririya a cikin zane gefen hanya kasan Tunfafiya, anan ne suka sanarwa manya aka zo domin a gani, a haka aka taru kan yarinyar ba a san wadanda suke jefar da ita a wurin ba. Kamar yadda majiyar ta shaidawa Managarciya.
Majiyar ta baiyana cewa an fahimci jaririyar sabuwar haihuwar ba ta da rai wanda ake ganin zafin rana ne ya yi mata yawa ya yi sanadin komawarta lahira.
Jinjirar da ke sanye da doguwar rigar sanyi mai hula an kasa fahimtar yanda aka yi aka kawo ta wurin aka jefar.
Ya ce hukumar makaranta sun nemi jami'an tsaro aka dauke jaririyar zuwa a asibiti in da aka tabbatar ba ta motsi.