An Kwantar Da Mataimakin Shugaban A Asibiti
An yi wa mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo tiyata a kafarsa a yau, bayan kwantar da shi a asibiti
Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar Laole Akande ne ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita, kamar yadda BBC ta rawaito.
Sanarwa ta ci gaba da cewa mataimakin shugaban kasar ya ji raunin ne yayin wasan sukwas (squash).
Nan gaba kadan ne a yau likitocinsa za su yi bayanin halin da yake ciki.
managarciya