Daga Awwal Umar Kontagora a Minna.
Alhamis din makon nan aka gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Neja, inda rahotanni suka nuna jama'a da dama sun yi biris da zaben wasu yankunan kananan hukumomi.
A karamar hukumar Rafi kuwa da ke daya daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro abin ya sha bamban domin jama'a sun yi tururuwa fitowa dan jefa kuri'arsu, Malam Bello Kagara da ya zanta da wakilin mu yace na fito tare da iyalina dan jefa kuri'a domin yancin mu ne mu zabi shugaban karamar hukuma da kansulan da zasu bada na su gudunmawa dan ganin an kawo mana zaman lafiya a karamar hukumar nan, tun kafin zabe ina daya daga cikin wadanda suka fito suna bin jama'a dan ganin kowa yayi zabe, kuma mun godewa Allah jama'a sun fito kuma mun jefa kuri'a lafiya ba tare da hargitsi ba.
Maganar cewar PDP ba ta cikin zaben, to ni ba dan jam'iyya ba ne, dan Rafi ne ka ga kuwa wata jam'iyya ba zata hana ni yanci na ba a matsayina na dan kasa ba, domin wadanda ke kai wa'adinsu zai kare watan gobe, in ban yi zaben ba wa zai jagorance mu.
Malam Ibrahim Balarabe ( Santurakin Kagara) kuma shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Neja, bayan jefa kuri'arsa ya bayyana ma wakilin mu cewar wannan zaben halastacce ne kuma yana bisa kan doka, dan haka na yabawa al'ummar Rafi wajen fitowa dan jefa kuri'a.
Bisa dokar zaben kananan hukumomi sha biyu zuwa sha biyar ga watan Disamba wa'adin wadanda ke kai zai kare, kuma babu hurumin yin gwamnatin rikon kwarya a kananan hukumomi, to ke nan wajibi ne a yi zabe, kuma kan idon ka yadda ka zagaya ka ga jama'a sun yi fiton dango wajen jefa kuri'unsu a dukkanin mazabun da hukumar zabe ta amince da su.
Maganar tsaro, gaskiya gwamna Abubakar Sani Bello da jami'an tsaro suna bakin kokarinsu, illa da me kamar yadda ka sani a dunke nan can na ballewa amma da yardar Allah matsalar tsaro ya kusa zama tarihi a yankin nan, domin matakan da gwamnati ya kamata ta dauka tana kan su yanzu haka wanda muna kyautata zaton nan da dan lokaci kadan kowani dan gudun hijira zai koma gidansa.
Hon. Ayuba Usman Katoko wanda tsohon sakataren hukumar ilimin bai daya ne kuma kafin shigarsa takara shi ne shugaban hukumar kula da shaye shayen barasa a jihar, shi ne dan takarar shugabancin karamar hukumar Rafi a jam'iyyar APC mai mulki, yace idan Allah ya ba shi nasara zai yi anfani da kwarewarsa da hanyoyi wajen samar da zaman lafiya a karamar hukumar Rafi.
Yace lallai akwai jan aiki a gaban mu, amma na san al'ummar mu masu kishi da son zaman lafiya ne, za mu hada kai wajen dakile duk wata barazanar rashin tsaro da yafi rike mana wuya a yanzu dan ganin yaran mu sun koma makarantun da ke rufe dan cigaba da karatu.
Zan yi anfani da wannan damar dan yin godiya ga maigirma gwamna wajen bada kulawarsa akan wannan matsalar da ke damun mu na tsaro, domin jajirtattun mutanen da ke zagaye da shi yan asalin karamar hukumar Rafi, ba su buge da bacci ba, a kowani lokaci idanun su da kunnen na gida dan sauraren al'ummar mu, dan haka ina mai jaddada wa gwamna karamar hukumar mu za ta cigaba da baiwa gwamnatin sa goyon baya dan ganin samun nasarar gwamnatin da jama'a suka zaba da hannun su.
Alhaji Bello Yakila, sakataren kudi na jam'iyyar APC, yace wannan zaben gwajin dafin manya zabuka ne na tafe, wanda al'ummar suka nuna gamsuwarsu da gwamnatin APC a jihar Neja.
A madadin uwar jam'iyya ta jiha ina jawo hankalin jama'a kowa ya kara rike kuri'arsa da kyau domin muna da sauran zabuka a gaba. Sannan jama'a su taimakawa gwamnati da jami'an tsaro wajen fallasa duk wata zaman lafiya a jihar nan, tabbas akwai kananan hukumomi da dama da ke fuskantar matsalar tsaro, amma ina da kwarin guiwar nan bada jimawa ba zai zama tarihi a jihar nan.
Koma da dai, kafin zaben an yi ta samun fargabar rashin yiwuwar zaben duba da yunkurin majalisar dokokin jihar na barazanar hana hukumar gudanar da zaben sakamakon zuwan jam'iyyar PDP kotu na ganin kotun ta dakatar da yin zaben bisa zargin zaben bai bisa ka'ida wanda ya kai a baya majalisar tayi barazanar korar shugaban hukumar zaben da sakatarensa na yin kunnen kashi da umurninta na dakatar da zaben kamar yadda ta umurta.
Masana dokoki dai, sun nuna karara cewar majalisar ba ta da wannan hurumin na dakatar wa ko nadi ga hukumar zaben, a cewarsu gwamna ne kadai zai yi umurtar majalisar tayi bincike akan korafi ko zargin laifi ga shugabannin hukumar tare da bada shawarar matakin da ya kamata a dauka bisa doka.
Malam Bello Kusharki, shi ne shugaban gamayyar jam'iyyun siyasar jihar ( IPAC), yace dukkan jam'iyyun siyasar jihar sun yarda da halascin zaben, kuma in ban da jam'iyyar PDP babu jam'iyyar da ba ta shiga zaben ba.
Zuwa yanzu dai jama'a na dakon jirar wadanda suka samu nasarar zaben daga shugabancin kananan hukumomi zuwa kansuloli wanda ake sa ran za a fitar ranar littinin din nan mai zuwa.