Na Samar da Sabon Salo Ne A Fim Igiyar Ƙasa Domin Inganta Harkar Wasan Hausa -- Darakta Basirou Nijar

Na Samar da Sabon Salo Ne A Fim Igiyar Ƙasa Domin Inganta Harkar Wasan Hausa -- Darakta Basirou Nijar

Na Samar da Sabon Salo Ne A Fim Igiyar Ƙasa Domin Inganta Harkar Wasan Hausa -- Darakta Basirou Nijar

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

A yunkurin da ake da shi na samar da ingantattun Finafinan Hausa masu inganci a duniya, Kamfanin shirya Finafinan Hausa mai suna 2N Media Produnction da ke Jamhuriyar Niger ta shirya wani Fim mai dogon zango mai suna 'Igiyar Ƙasa' da ake ganin ya zo da sabon salo da kuma ingancin labari,

Babban Darakta kuma marubucin Fim din Basirou Garba, a tattaunawar mu da shi ya bayyana cewa, an daɗe ana aikin gyara labarin kafin a fara daukar shi, ba don komai ba sai don a samar da nagartaccen labari, 

Ya ƙara da cewa " yawan karanci karancin littafai da kallon finafinan ne yasa na kirkiro labarin kuma na bada umurnin a wannan Fim Igiyar Ƙasa"

"Kuma babbar manufar Fim din shi ne mu nuna  alaƙar mutum da sauran ƙwari, Maciji ne bai cutar ba amma sai aka fara cutar da shi to amma a kokarin daukar fansa sai ya yi kuskure ta yadda bayan ya gama daukar fansar sai ya gane cewa  akwai kurakurai"

Darakta Basirou ya cigaba cewa " na yi iya kokari na a matsayina na Darakta na siffanta kwaron a matsayin Aljani  ba mutum ba, na kuma siffanta dabi'arsa da ta mutane, don haka ni Fim din Igiyar Ƙasa babbar nasara ce a guri na".

Shi ma Furodusan Fim din  Saminu A. Turaki "Mun samu ƙalubale da yawa a Fim din nan amma gaskiya mun sami nasarori masu dimbin yawa, domin bayan rubuta labarin sai da mukai wata 17 muna duba labarin muna gyare-gyare"

Kazalika ya kara da cewa  da cewa "Fatan da na ke da shi ga wannan Fim din shi ne ya zama an nuna shi ga tashoshin Talabijin na duniya domin a ga irin aikin da muka yi, kuma duk inda ake shiga gasa ta duniya za mu yi kokari mu shiga muna fanan samun sakamako mai kyau". a cewar Furodusa Saminu Turaki