Tinubu ya Naɗa Kulu Haruna da wasu mutane sama da 30 a matsayin jakadun Najeriya 

Tinubu ya Naɗa Kulu Haruna da wasu mutane sama da 30 a matsayin jakadun Najeriya 

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sabon rukuni na manyan jakadu  wanda ya haɗa da wasu manyan tsoffin jami’an gwamnati da hafsoshin tsaro.

A cikin jerin sunayen da aka fitar, shugaba Tinubu ya naɗa Ibok-Ete Ekwe Ibas, tsohon shugaban rundunar sojin ruwa kuma tsohon kantoman riko   na jihar Rivers, a matsayin babban jakada.

Haka kuma, shugaban ƙasar ya naɗa Abdulrahman Dambazau, tsohon Ministan Harkokin Ciki da tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, a cikin jerin sabbin jakadun.

Wasu da aka ƙara sun haɗa da tsohon sanata Ita Enang da Chioma Ohakim, tsohuwar uwargidan gwamnan jihar Imo.

Wannan na zama rukuni na uku na jakadu da gwamnatin Tinubu ta sanar tun bayan fara wa’adin mulkinsa.