2027: Ba ido rufe ADC ke neman mulkin Nijeriya ba— David Mark 

2027: Ba ido rufe ADC ke neman mulkin Nijeriya ba— David Mark 

Shugaban jam’iyyar ADC, David Mark, ya ce manufar jam’iyyarsa ba wai neman mulki ido rufe ba ne, illa dai hidima ga ‘yan Najeriya.

Da yake jawabi a taron farko na kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar a Abuja, Mark ya ce ADC an kafa ta ne domin gina ƙasa mai adalci da damar ci gaba ga kowa da kowa.

Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta zama mai gaskiya, ladabi da gaskiya a shugabanci, tare da tabbatar da cewa cancanta tafi biyayya a mukamai.

Mark ya kuma ce ADC za ta tabbatar da gudanar da zaɓe mai tsafta da ingantaccen tsarin rajista ta Internet da wallafa rahoton ayyuka duk bayan wata uku.

Ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta kare tsarin raba iko, ƙarfafa majalisu da kotuna, da tabbatar da adalci ga kowa.

"Ba mu neman mulki don son rai, muna neman shi ne don gina  mutunci da ‘ya’yanmu za su alfahari da shi,” in ji Mark.

Ya ce ADC za ta tallafa wa manoma da ƙananan ‘yan kasuwa, da tabbatar da gaskiya a kashe kuɗaɗen gwamnati, tare da tabbatar da cewa jama’a sun fi kome muhimmanci.