Ɗan Wasan Hausa Sani Garba S.K Ya Rasu
Allah Ya yi wa fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa Sani Garba SK rasuwa a yau Laraba a birnin Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya
Wani fitaccen furodusa Abdul M Amart Mai Kwashewa ne ya tabbatar wa da BBC rasuwar ɗan wasan.
Marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke Nasarawa a ranar Laraba da yamma.
"Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan inda ya shafe mako biyar yana jinya a asibitin," in ji Amart.
A kwanan baya margayin ya musanya batun rasuwarsa da kansa sai yau ga shi Allah ya karɓi rayuwarsa.
'Yan wasan Hausa za su yi jiname rashin ɗan uwansu a wannan lokacin da suke buƙatar irinsa a cikinsu.
managarciya