Sanata Tambuwal ya kadu da rasuwar 'yar Kannywood Daso

Sanata Tambuwal ya kadu da rasuwar 'yar Kannywood Daso
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya yi alhinin rasuwar 'yar wadan Hausa Hajiya Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso.
A bayanin da ya wallafa a turakarsa ta Facebook Tambuwal ya ce "na samu kaina cikin kaduwa da alhinin rasuwar fitacciyar jarumar fina-finanai a masana'antar Kannywood Hajiya Saratu Gidado (Daso), wadda ko a ajiya tana rayuwa kamar kowa.
"A tsawon rayuwarta, Daso ta yi amfani da basirarta da fasaharta wajen sanya farin ciki a fuskokin miliyoyin iyalai da kuma nishadantarwa a shafukanta na sada zumunta," kalaman Sanata Tambuwal.
Sanata ya ce rasuwarta ba rashi ne kawai ga danginta kadai ba, babban rashi ne ga masana'antar fasahar kwaikwayo da ma kasa baki daya.
Allah ya gafarta ma ta kura-kuranta ya sa aljanna ce makomarta.
"Ni da ta iyalina muna mika ta'aziyya ga danginta, da masana'antar Kannywood.
"A karshe Ina addu'a Allah ya baiwa iyalai da 'yan uwa hakurin jure wannan rashi."