Yadda Za Ki Hada Farfesun Ganda

Yadda Za Ki Hada Farfesun Ganda
MOMMYN MUS'AB   CLASSIC FOOD
                 & 
  GYARAN JIKI
    
Yadda Za Ki Hada Farfesun Ganda
 
*TARBIYYAR YARA& ordinary food*
 
Farfesun Ganda
 
Kayan Hadi
 
• Ganda
•Attarugu
•Albasa
•Tumatiri
• Nutmeg
•Tafarnuwa
•Maggi
• kori
• Kayan kamshi
• Tukunyar dafa ganda (Pressure cooker)
 
Hadi
*Bayan uwargida ta wanke ganda da ruwan kanwa domin cire karni, sai ta zuba a tukunyar dafa ganda* *domin samun farfesu mai laushi . Sai ta yayyanka albasa da tumatiri. Ta jajjaga attarugu daidai misali datafarnuwa. Sai ta daka garin nutmeg ta zuba da maggi da kori da thyme.* *Sannan sai ta zuba ruwa daidai misali ta rufe. Sai ta jira ya nuna na tsawon awa daya. Sannan ta sauke.*
 
*Ana son cin wannan girkin da safe ko da dare. Wannan irin girki, shi ne, wanda ya fi dacewa da masu son rage kiba. Domin ganda ba ta dauke da sinadarin dada kiba, illa a ci kawai don dadi. Tafarnuwar da aka sanya a cikin girkin na rage mura da kuma kare wadansucututtuka kamar su mura da sanyi da sauransu. Ana son a rika girka irin wannan girki ga*
*maijego, domin samun ruwan nono da karin koshin lafiya. Da fatan wannan girki zai sanya kunnen mai gida motsi. Ga dadi ga kuma arhar kayan girki. A sha lagwada lafiya*
 
Mommyn Mus'ab
 
Gamasu bukatar shiga abude yake
 
07041105956
 
Share✅
Edit❌
Comment✅