Akwai Lokacin Da Na Yi Dana Sanin Fara Wasan Hausa---Hauwa'u Salga

Akwai Lokacin Da Na Yi Dana Sanin Fara Wasan Hausa---Hauwa'u Salga
 

Daga Hauwa'u Salisu(Haupha)

 
Muna son jin cikakken sunan jarumar da garin da aka haife ta da inda ta yi karatu!
 
Da farko sunana Hauwa'u Abubakar Salga  ana kira na da Amirah  an haife ni a kano unguwar filin Dantata na yi primary school a Ahababun Mariya Batam Na kammala na yi junior a filin durmi daga nan na wuce senior Masaka dake Gwammaja. To Allah bai bani damar cigaba da karatu ba. 
 
 
Tau jaruma Hauwa'u za mu so mu ji wane irin abinci da tufafi kika fi sha'awa, sannan  wane irin tufafi ne baya burge ki, haka wane irin abinci ne baki so?
 
 Tau ni dai ina son golden color, abinci kuma nafisan taliya, kuma babu kalar abincin da bana ci.
 
 Lallai ba ki wahalar baƙunta tunda kina cin komai 
 
Haka ne wannan
 
 Game da sutura fa manya ko ƙanana wane kika fi sawa?
 
Mayan kaya nafi sawa nafi jin dadinsu
 
Shin yaushe ne jarumar ta tsunduma harkar fina-finai, Wane ƙalubale ta fuskanta kafin ta fara harkar fim?
 
Yanzu wajen shekara biyu na fara a gida ba'a sani ba saboda Mamana a lokacin ta yi tafiya tau dama  wani da muke magana da shi Dan Gwammaja ne sunanansa Sadiq sai ya ce min za su je aikin kwana 90 na ce  tau a lokacin na fara shiga Camera Mamana da ta dawo nake fada mata naje aiki, a lokacin ta yi min duka bayan wata biyu aka saki aiki kannen babana suka zo su da yawa har da wanda ban san su ba, gaskiya ranar na yi dana sani sosai, dan nadaku awajansu suka ce su ba za su yarda ba, sai sun kai wanda yakai ni Kara dakyar suka hakura. Daga baya dai da suka ga a haka ina satar hanya naje wajan aiki sai suka hakura suka zuba min ido tau Alhmulillah yanzu sai godiya gaskiya.
 
 
 
Jaruma Hauwa'u da kika fara Film ko akwai wani cikas ko matsala da kika samu a gun abokan aikinki, misali ana yawan cewa manyan ku na danne yaran suna ci masu mutunci wasu ma ance har baɗala suke da na ƙasa da su idan za su saka su a aikin Film  shin ke baki fuskanci irin wannan matsalar ba? 
 
Eh to gaskiya kowace sana'a akwai na banza haka akwai nagari ni dai ban samu wannan kalubalan ba, na samu dai Wanda zaka je aiki ko kudin mota baza'a baka ba haka zaka je Ka dawo gashi ba magana mai dadi kaikuma a gida kace ka tafi aiki dole sai dai na dauka a kudina na nuna amatsayin kudin aiki ne.
 
Ya sunan Film ɗin ki na farko?
 
Suna film Dina Na farko So Da Hawaye
 
Zuwa yanzu Film nawa ki kai? 
 
Gaskiya zuwa yanzu ban san adadin wadda na yi ba saboda akwai wanda kai ka ja aikin akwai wadda za'a kira ka ka yi sin daya ko biyu yadanganta. 
 
Waye ubangidanki a harkar Film?
 
A yanzu ubangidana a kannywood sunansa Abubakar G. Boy
 
 
 
 
A yanzu maganar da ake ko akwai niyyar aure ga jarumar, 
domin ance jarumai mata ba su aure shin  gaskiya ne?
 
A'a ba gaskiya ba ne shi aure nufi ne na Allah da kuma lokaci, idan lokacin abu ya kare wallahi dole ku rabu duk son da kake wa mutum haka rayuwa take.
 
To akwai wanda ke ƙasa ma'ana wanda ku kai alƙawarin aure da shi?
 
Eh akwai in Allah ya amince.
 
 
 Da kika ga hakan(ana yi maki kora da hali) sai kika sauya waje koko dai kin cigaba ne saboda kina son ki kai matakin nasara a harkar?
 
A'a hakura na yi na cigaba gashi yanzu sai labari.
 
Wane Film ne kike yi yanzu haka wanda kike kan aikinsa?
 
 Sunan film din Majanunin So
 
Kina cikin Film ɗin MATAKIN NASARA za mu so jin yadda labarin yake watau muna son jin dogo ne ko gajere kuma nawa ye Film ɗin, wane mataki kika fito a cikin Film ɗin, ya fita ko yana hanya dai
 
......... muna hanya dogon zango ne producer shi ne Asasanta.