Matasa Sun Yi Yunƙurin Hana Ɗan Majalisa Shiga Jakusko A Yobe
Daga Muhammad Maitela, Yobe.
Xan majalisa mai wakiltar qananan hukumomin Bade da Jakusko a jihar Yobe, Hon. Zakari Ya'u Galadima ya gamu da fushin fusatattun matasan yankin sa, inda suka yi qoqarin hana shi shiga garin Jakusko, shalkwatar qaramar hukumar, a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaven fidda-gwani.
Al'amarin ya faru ne ranar Talata, a lokacin da matasan suka yi qoqarin hana xan majalisar shiga garin Jakusko ya wuce Gashuwa, yankin da yake wakilta a zauren majalisar wakilan Nijeriya. Wanda su ka fara yin zanga-zanga tare da qona tayoyin a kan titunan da zai wuce tare da yi masa ihun ba ma so, wasu kuma xauke da duwatsu suna jifar motocin sa.
Wata majiya a garin Jakusko ta shaida wa wakilinmu cewa, matasan sun xauki matakin ne biyo bayan dogon lokacin da xan majalisar ya xauka bai kai ziyara a yankin nasa ba balle ya san matsalolin da al'ummar da yake wakilta.
"Yau kimanin sama da shekara biyu Hon. Zakari Ya'u Galadima bai leqa yankin Bade/Jakusko ba, sannan dukan abubuwan da ke faruwa a yankin basu dame shi ba, sannan an sha kai qorafi ga na sama domin ya gyara abin ya faskara. Amma saboda tsabar rashin ta-ido, ya ga lokacin zave ya zo, shi ne babu kunya ba tsoron Allah ya xauko qafa a sake zavarsa; tunanin sa shi ne ya bayar da kuxi tare da samun xaurin gindin gwamnati."
"Amma a wannan karon, jama'a sun gaji da irin wannan baqin mulki wanda yake yi wa jama'a. Kuma ko da ace ita ma gwamnatin babu yadda za a yi ta tilasta wa al'umma abin da ba sa buqata. Amma idan ya na ganin wannan zai yuwu; ga fili ga mai doki. Kuma matakin da waxannan matasa suka xauka saqo ne zuwa gareshi da waxanda yake ganin zasu qwaci mulkin su bashi." Ta bakin majiyar.
Bugu da qari kuma, shima wani xaya daga cikin dattawan Jakusko (ya bukaci a sakaya sunan shi) ya shaida wa wakilinmu cewa, "Ko shakka babu al'ummar Bade da Jakusko sun gaji da salon wakilcin Hon. Zakari Ya'u Galadima, saboda rashin tavuka abin a zo a gani savanin yadda muke jin takwarorin sa a wasu jihohi suna yi. Wallahi mun gaji da wakilcin sa, kuma matiqar masu faxa aji a siyasa da gwamnati suka kafe sai shi, to ko shakka babu jam'iyyar PDP na iya cin kujerar Bade/Jakusko."
"Saboda haka muna kira ga Maigirma Gwamna Buni tare da shugabanin jam'iyyar APC su kawo wa mazabar Bade/Jakusko xauki. Jama'a sun gaji da salon wakilcin Hon. Zakari Ya'u Galadima, saboda ya kasa tavuka komai, sannan uwa uba ayyukansa ya nuna cewa ba zai iya ba, ya dace a canja mana da sabin jini mai qwazo." Ya nanata.
Duk qoqarin da wakilinmu ya yi wajen jin ta-bakin Hon. Zakari Ya'u Galadima ko wani makusancin sa abin ya ci tura; an buga wayarsa sau-shurin masaqi ba a xagawa, tare da tura saqon kar-ta-kwana shima babu amsa.
managarciya