Kara Lokacin Rijistar Katin Zabe Dama Ce Ga Al'ummar Yobe----Hon. Shariff Abdullahi

Kara Lokacin Rijistar Katin Zabe Dama Ce Ga Al'ummar Yobe----Hon. Shariff Abdullahi
 
Daga Muhammad Shamsudeen, Yobe.
 
Dan takarar kujerar Gwamnan jihar Yobe a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Hon. Shariff Abdullahi ya yaba da matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dauaka na kara wa'adin rijistar katin zabe zuwa karshen watan June, 2022. Tare da kira ga ilahirin al'ummar jihar Yobe da kasa baki daya su yi amfani da wannan dama.
 
Ya sanar da hakan a takardar manema labaru mai dauke da sa-hannun sa, tare da bayyana cewa, "mun yaba wa matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dauaka na kara lokacin rijistar zabe zuwa karshen June 2022 babbar dama ce ga al'ummar Jihar Yobe da kasa baki daya, kuma nasara ce ga tsarin dimukursdiyya."
 
Hon. Abdullahi ya ce sanin kowa ne cewa sai ta hanyar katin zabe ne al'ummar jihar take da cikakkiyar damar kawo sauyi mai ma'ana a Yobe da Nijeriya, tare da canja gwamnatin da ta kasa inganta rayuwar jama'a zuwa gwamnati mai kwazo ta kishin al'umma. 
 
Ya ce, "Saboda haka, wannan dama ce ga al'ummar mu, kuri'armu ita ce yancinmu kuma damar da zamu yi amfani da ita wajen kawo shugabanin da zasu tausaya mana tare da ciyar da jiharmu gaba, ta bunkasa."
 
"Muna kira ga ilahirin al'ummar mu, su fito kwansu da kwarkwata, maza da mata wadanda shekarun su suka kai, su hanzarta zuwa cibiyoyin sabunta katin zaben, domin su karba kuma su zabi jam'iyyar PDP domin ci gaba da muhimman ayyukan da ta saka a gaba."
 
"Kar mu manta, zaben shugabani nagari wajibi ne ga kowane mutum mai kishin kasarsa da al'ummar sa, kuma damar yin hakan ya rataya ne idan kana da katin zabe. Al'ummar jihar Yobe dama ce garemu wadda ya dace muyi amfani da ita." Ya nanata.