Matasa Sun Fusata da Kashe Ɗan Uwansu, Sun Bankawa Fadar Basarake Wuta a Arewa 

Matasa Sun Fusata da Kashe Ɗan Uwansu, Sun Bankawa Fadar Basarake Wuta a Arewa 

 

Wasu fusatattun matasa a sun kona fadar Hakimin Lere da ke karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi. Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun bankawa fadar wuta ne sakamakon rikicin da ya faru tsakanin sojoji da magoya bayan jam'iyyar PDP na garin Lere. 

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, sojojin sun kashe mutum ɗaya, Habibu Aminu yayin da wasu mutane shida kuma suka samu raunuka. 
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin ta hannun mai magana da yawunta, SP Ahmed Wakili. 
Wani mazaunin Lere da aka harba a ido lokacin da sojojin suka kai samame, Zaharedden Mohammed, ya ce matasa sun ƙona fadar ne kan zargin da suke wa hakimi. 
A cewarsa, fusatattun matasan sun taɓa fadar basaraken bisa zargin shi ya sa sojoji su sanya dokar zaman gida a yankin, rahoton Daily Post. 
"Wasu daga cikin matasan tawagar kamfen PDP suna takun saƙa da sojoji, wannan ya sa sojojin suka fake da dokar hana fita domin su farmaki wasu mutane."