Sallah: Matsalar tsaro da talauci za su zama tarihi a Nijeriya----Sarkin Musulmi

Sallah: Matsalar tsaro da talauci za su zama tarihi a Nijeriya----Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya yi hasashen Matslar tsaro da talauci da suka addabi al'umma za su zama tarihi a Nijeriya matukar gwamnati ta ci gaba da yin abin da ya dace ga jama'ar da ake shugabanci.

Sarkin Musulmi a jawabinsa na barka da sallah da ya gabatar ga al'ummar Musulmi a fadarsa bayan kammala sallar idi ya ce rashin tsaro da talauci da ke addabarmu za a kawar da shi.
Ya yi kira ga mutane su nemi ilmin addini dana zamani domin hakan ne kawai zai samar da cigaba a cikin jama'a.
Sa'ad Abubakar ya godewa malaman addini yanda suka gudanar tafsirin azumin bana cikin nutsuwa ba tare da fadin wasu kalmomi marar dadi da cin zarafi ba.
"Hakan abin yabawa ne malamai su cigaba da mutunta juna a wurin wa'azi da karance-karancensu".