Ramadan: Majalisar dokokin Sokoto ta umarci Gwamnati ta yi gyara kan ciyarwar

Ramadan: Majalisar dokokin Sokoto ta umarci Gwamnati ta yi gyara kan ciyarwar
 
Majalisar dokokin jihar Sakkwato ta 10, ta shawarci Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu ta fadada ciyarwar azumin Ramadan da gwamnati ke yi a kwaryar birni zuwa kananan hukumomi 23 na jihar.
A zaman majalisa wanda shugabanta Tukur Bala Bodinga ya jagoranta sun saurari bukatar da dan majalisa Mai wakiltar mazabar Tambuwal ta Gabas Bashir Isa Jabo ya gabatar in da Kabiru Dauda na mazabar Gada ta Gabas ya goyi bayansa.
Kudirin wanda majalisa ta bayyana abu ne Mai muhimmanci da ake bukata da gaggawa, ciyar da abinci ga masu azumi da gwamnati ke yi a duk shekara cikin kwaryar birnin jiha akwai bukatar ta fadada shi ya zagaye dukkan kananan hukumomin Sakkwato, duba da halin da ake ciki na matsin rayuwa, dukkan sako da lungu na cikin al'umma ana fuskantar wahala da matsi.
Majalisa na ganin aiwatar da hakan zai samar da saukin rayuwa a cikin jama'ar karkara musamman wadanda ba su da abin da za su ci a lokacin buda baki.
'Yan majalisa gaba daya sun amince gwamnatin jiha ta fadada ciyarwar azumin Ramadan a zagaye dukkan kananan hukumomin Sakkwato.