Hukumar Kwastam Za Su Buɗe Boda Domin Shigo Da Abinci Daga Ƙasashen Waje Daga Sati Mai Zuwa
Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta sanar da cewa dokar dage haraji kan kan kayayyakin abinci da magunguna za ta za fara aiki a mako mai zuwa.
Sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban hukumar Kwastam Bashir Adeniyi a wata hirarsa da manema labarai.
Hakan na nufin masu shigo da kayayayyakin abinci kamar shinkafa, Alkama, Masara, Dawa da sauran hatsi, ba za su biya haraji ba har tsayin watanni uku.
Wannan tsarin ya biyo bayan kudirin Gwamnatin shugaban Tinubu na rage farashin kayan abinci don rage wa ‘yan kasa radadin tattalin arziki.
Daga Aliyu Samba
managarciya