Maniru  Ɗan'iya/Yusuf Sulaiman: Kwamitin da Gwamnatin Sokoto ta kafa ya saɓa alƙawali

Maniru  Ɗan'iya/Yusuf Sulaiman: Kwamitin da Gwamnatin Sokoto ta kafa ya saɓa alƙawali

 

Kwamitin da  Gwamnatin Sakkwato karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ta kafa kan bincikar yadda tsohuwar gwamnatin jiha karkashin kulawar Sanaata Aminu Waziri Tambuwal ta gudanar da mulkinta, ta yi aabin da ba a saba gani ba a sauraren bahasin da take yi.

Kwamitin ya gayyaci tsohon mataimakin Gwamnan jiha Alhaji Manir Muhammad Dan’iya da tsohon Ministan Sufuri da su bayyana gabanta a ranar 22 ga watan Mayun 2023, da safe, sun amsa gayyatar a dakin da ake gudanar da sauraron bahasin, ba ko mutum daya daga cikin mutanen kwamitin.

Yusuf  Suleiman bayan sun gama jiran mambobin kwamitin ba su zo ba, ya yiwa Managarciya  bayani ya ce hakan ya nuna da gangan aka yi wannan shi ne karo na biyu da suke yi mana haka, bai kamata su rika wasa da hankalinmu ba.

Ya ce bita da kullin siyasa a siyasance  bai kamata ba, cin dunduniyar abokin hamayya ba zai taimaki siyasa ba domin in Kai ne yau gobe ba kai ba ne.

"Ko da suka gayyace ni bana Sokoto amma saboda na girmama kwamitin da doka ta samar na bar Abuja a jiya(Talata) na sauka Birnin Kebbi domin ba jirgin da zai zo Sokoto, gashi mutanen nan ba wannda ya zo.

"Ina kira gare su kar su bari a yi amfani da su domin cin zarafin wasu, mambobin kwamitin mutane ne da ake ganin girmansu a cikin jama'a su rike kimarsu."

Dan Amar na Sokoto ya ce in har kwamitin ya san ba zai yi zama ba sai ya sanar da mu ba wai mu zo ba mu same su ba, tsohon mataimakin gwamna da tsohon minista ba kananan mutane ba ne a matakin jiha da kasa baki daya.

Ya ce in har ina gari suka kara gayyata ta  zan karba domin ba da bahasin abin da suka nema.

Duk yunkurin jin ta bakin sakataren kwamitin wanda shi ne Kwamishinan shari'a a jihar Sokoto lamarin ya faskara.