Gwamnatin Buhari Ta Baiwa Daliban Jami'a Shawarar Matakin Da Za Su Dauka Kan ASUU

Gwamnatin Buhari Ta Baiwa Daliban Jami'a Shawarar Matakin Da Za Su Dauka Kan ASUU
 

Ministan Ilimi a Najeriya, Adamu Adamu, a ranar Alhamis, ya ce alhakin kungiyar malaman jami’o’i ne ta biya daliban jami'a diyyar lokacin da suka bata yayin yajin aikin na watanni shida na ASUU ba gwamnatin tarayya ba. 

Ya kuma ce gwamnati ba za ta amince da bukatar kungiyar na biyan malamai kudaden alawus-alawus din su na tsawon watanni shida da suka bata ba tare da aikin karantarwa ba.
Adamu ya ba da shawarar cewa daliban da abin ya shafa su kai ASUU kotu domin neman diyya bisa lokacin da kungiyar ta bata musu yayin yajin aikin. 
Ministan Ilimin ya bayyana haka ne a wajen zama na 47 na taron manema labarai na Majalisar Dokokin Kasa da tawagar Shugaban kasa kan sadarwa ta shirya a fadar Aso Rock Villa, Abuja. 
A cewarsa, gwamnatin tarayya ba ta da wani dalili ko alhakin biyan miliyoyin daliban da aka sanya a tasku na tsawon watanni shida saboda da sunan yaji. 
Ya kuma ce idan daliban sun kuduri aniyar neman diyya to su gurfanar da ASUU a kotu.