Mutun 5 sun rasu a lokacin da suke raka gawar mai Kwalara a Sokoto

Mutun 5 sun rasu a lokacin da suke raka gawar mai Kwalara a Sokoto

Mutun 5 sun rasu a lokacin da suke raka gawar mai Kwalara a Sokoto

Mutum biyar sun riga mu gidan gaskiya dukkansu ‘yan uwan juna ne a saman hanyarsu daga Lagos zuwa Sakkwato in da suka yi wa gawar mai cutar Kwalara rakiya domin kawo ta gida a yi mata sutura.

Margayan dukkansu ‘yanci rani ne dake zuwa Jihar Legas yin nema  lokaci zuwa lokaci in aka samo a dawo wurin dangin daga bisani a koma.

Aminiya ta samu bayanin cewa mutanen da bin ya ritsa da su na zaune ne a garin Ijeota, yankin da cutar ta kwalara ta fi kamari a Jihar Legas.

Daya daga cikinsu ne ya fara kamuwa da cutar, kuma take ta kashe shi cikin dan kankanin lokaci.

“Bayan rasuwarsa sai ’yan uwan nasa suka yanke shawarar mayar da gawarsa zuwa gida a  garin Sanyinna dake Karamar Hukumar Tambuwal a Jihar Sakkwato don yi masa jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

“Suka dauki hayar bas zuwa Sakkwato, a kan hanyarsu ne mutum biyar suka sake rasuwar bayan sun kamu da cutar kafinsu iso cikin dangin da ke jiran gawar dayan da ya fara cikawa.

“Yanzu haka an kwantar da wasu mutum biyar daga cikin fasinjojin da suka kamu da cutar ta kwalarar a karamar asibitin Sanyinna.

“An hana motar shiga garin, mun sanar da  direban da ya wuce kai tsaye zuwa asibiti kuma hakan ya yi lokacin da suka iso garin Sanyinna” a cewar wata majiya.

Ardon garin Sanyinna, wanda shi ne uban kasar yankin  Alhaji Shehu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin,  ya ce wadanda suka rasun sun baro Legas ne zuwa Sakkwato.

Ya kara da cewa an yi musu sutura tare da binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.