Matsalar tsaro: Matasa sun kone gidan kwamishinan tsaro na jihar Sokoto

A satin nan ne suka  kone gidaje biyu na Kwamishinan ma'aikatar tsaro na jihar Sakkwato Kanal Garba Moyi Isa, suka je gidan Sarkin Gobir na Isa aka farfasa motocin alfarma dake cikin gidansa da lalata fadarsa kan zarginsu da kasa daukar matakin da yakamata kan 'yan bindiga dake yin tu'anati ba dare ba rana.

Matsalar tsaro: Matasa sun kone gidan kwamishinan tsaro na jihar Sokoto

Wasu gungun matasa a karamar hukumar Isa a jihar Sakkwato sun fusata kan matsalar tsaron da yankinsu yake ciki kuma suna ganin kamar shugabanni a karamar hukumar ba su damu da halin da ake ciki ba domin suna tafiya cikin birnin jiha su yi zamansu hakan ya sa suka yi gangami nuna fushi.

A satin nan ne suka  kone gidaje biyu na Kwamishinan ma'aikatar tsaro na jihar Sakkwato Kanal Garba Moyi Isa, suka je gidan Sarkin Gobir na Isa aka farfasa motocin alfarma dake cikin gidansa da lalata fadarsa kan zarginsu da kasa daukar matakin da yakamata kan 'yan bindiga dake yin tu'anati ba dare ba rana.

Bashir Altine Guyawa dan asalin Isa ne ya ce abin da ya sanya matasan suka yi haka fushi ne suka yi kan matsalar saron da ake fama da ita a garin kuma ba wani yunkuri da suka ga shugabannin na yi.

Sarkin Gobir na Isa Alhaji Nasiru Ahmad na biyu wanda aka bubbuge fadarsa ya ce "In ma sun ce ba mu yi komai ba, a kan tsaronsu Allah ya sani, yanzu shekara ta 13 a sarautar nan, amma ba wani mutum da zai ga wanda Sarkin Gobir ya zalunta naira 10, balle na sa hannu a wani abu da yake na haramci da ba mai kyau ba, bana fatar hakan nan."

Ya ce su sarakuna aikinsu a yanzu bayar da labari kan kaza ya faru kuma yana yi ga hukumomi.

Kwamishinan tsaron da aka kone gidajensa biyu ya ce ba zai yi magana ba domin hukumar 'yan sanda na bincike kan lamarin.

Shugaban karamar hukumar na Isa Alhaji Yusuf Dan'ali ya gayawa Aminiya cewa bai san dalilin da ya sanya mutanen suka yi haka ba domin ba a sanar da shi ko tuntubarsa kafin aiwatar da gangamin ba.

"Abin da nasani nauyin da aka dauramin matsayin shugaba ina kan kokarina, in ka duba muna kan kokarin shawo kan matsalar nan da ya sa suka yi haka a karamar hukuma da jiha."a cewarsa.

Dan Ali ya ce har yanzu ba a san adadin hasarar da aka yi ba, kwamishin 'yan sanda ya zagaya a gidan Kanal Moyi da Sarkin Gabas, yanzu ana kan binciken lamarin.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce muna kan bincike akai kuma an fara kama wadan da suka yi lamarin.