Jami'an tsaron Farin kaya DSS sun mamaye fadar Sarkin Kano a daidai lokacin da ake Ya'da Jita jitar tsige Sarkin

Jami'an tsaron Farin kaya DSS sun mamaye fadar Sarkin Kano a daidai lokacin da ake Ya'da Jita jitar tsige Sarkin

A yau ranar Alhamis wasu jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) suka mamaye fadar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a daidai lokacin da jita-jitar tsige Sarkin ta yi katutu.

Wannan na zuwa ne a bayan amincewar dokar da majalisar dokokin jihar Kano ta yi na gyara dokar (sakewa doka), 2024 da majalisar dokokin jihar ta yi a safiyar ranar Alhamis.

Wakilinmu da ya ziyarci fadar da misalin karfe 11 na safe, ya ga wasu jami’an DSS da aka girke a fadar.

Ko da yake an ce Sarkin Kano ya je jihar Ogun ne a wata ziyarar sirri da ya kai Awujale na Ijebuland, Oba Sikiru Kayode Adetona, an ga jami’an tsaro a kofar fadar suna jiran ko wane hali.

Dokar ta soke dukkanin ofisoshin da aka kafa a karkashin dokar da aka soke kuma idan Gwamna Abba Kabiru Yusuf ya amince da shi, ya zama doka kuma akwai jita-jita cewa za a iya tsige sarkin.

Kudirin da aka amince da shi ya tanadi cewa gwamnan zai dauki dukkan matakan da suka dace domin mayar da masarautar Kano matsayinta na baya kafin a kafa dokar da aka soke.