Makarantar Almajirrai ta Gwamnatin Tarayya Kwalliya Ba Ta Biya Kuɗin Sabulu Ba

Jonathan ya cika alkawallin   a ranar talata goma ga watan Afrilu na shekarar 2012  ya kaddamar da  makarantar tsangaya da za ta  gwamaya ilmin islamiya dana boko ta kwana irinta  ta farko a garin Gagi cikin karamar hukumar Sakkwato ta kudu, a jihar Sakkwato. Za a gina sauran irin wannan makarantar har guda 34 a ragowar jihohin Arewa da kuma a garin Auchi na jihar Edo. Shi dai wannan aikin a baki dayansa zai lakumewa gwamnatin tarayya kudade naira miliyan dubu biyar a lokacin. Makarantar wadda aka  kaddamar  a jihar Sakkwato ta kunshi rukunin azuzuwa sha biyar da dakunan kula da bincike harsuna dana harda Alkur’ani dana karawa juna sani akan sana’o’i da gidajen kwanan malamai kazalika da kuma babban dakin cin abancin dalibai.

Makarantar Almajirrai ta Gwamnatin Tarayya Kwalliya Ba Ta Biya Kuɗin Sabulu Ba

Tsohon  shugaban kasa Goodluck Jonathan  a lokacin yakin neman zabensa na 2011  ya yi alkawalin shawo kan harkar barace-baracen yara kanana  ta hanyar gina makarantun almajirai na kwana irin na zamani a fadin jihohin Arewa 18 in ban da jihar Filato,domin tsugunar da almajiran da yawansu ya kai kimanin   miliyan tara.

Jonathan ya cika alkawallin   a ranar talata goma ga watan Afrilu na shekarar 2012  ya kaddamar da  makarantar tsangaya da za ta  gwamaya ilmin islamiya dana boko ta kwana irinta  ta farko a garin Gagi cikin karamar hukumar Sakkwato ta kudu, a jihar Sakkwato. Za a gina sauran irin wannan makarantar har guda 34 a ragowar jihohin Arewa da kuma a garin Auchi na jihar Edo.</p

Shi dai wannan aikin a baki dayansa zai lakumewa gwamnatin tarayya kudade naira miliyan dubu biyar a lokacin.

Makarantar wadda aka  kaddamar  a jihar Sakkwato ta kunshi rukunin azuzuwa sha biyar da dakunan kula da bincike harsuna dana harda Alkur’ani dana karawa juna sani akan sana’o’i da gidajen kwanan malamai kazalika da kuma babban dakin cin abancin dalibai.

 A jawabinsa wajen bukin kaddamar da makarantar, gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko a lokacin ya  godewa Jonathan kan  gina wannan makarantar da ya yi,tare da yi masa alkawalin kulawa da makarantar yadda yakamata domin tabbatar da dorewarta. Hakama  ya kara da cewar  zai baiwa shugabannin kananan hukumomi 23 dake jihar kwarin gwiwar kafa ire-iren wadannan makarantun a yankunansu daban-daban.

A nasa kalamai, sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya bayyana cewar,wannan makarantar ko shakka babu za ta taimaka wajen magance matsalar almajirai da yankin na Arewa ya jima yana fama da su, ya kuma yi kira ga uwaye da su bayar da cikakkken hadin kansu,kasncewar ilmin islamiya dana boko su ne muhimman gadon da za a iya bar wa ‘ya’yansu.

 

Shugaban makarantar na farko Malam Ubaidullahi Shehu Garge, a zantawar da ya yi da wakilinmu, a lokacin da aka bude makarantar ya bayyana yadda gwamnati ta tsara shirin don samun  samu nasara, “Yanzu mun fara da dalibai 50 da aka dauko a fadin jihar nan kowace karamar hukuma almajiri biyu ne kacal aka dauko,kafin shigo da sauran yaran,a bangaren malamai kuwa an dauko malamin zaure  biyu,dana boko  da dama,don ka san ba zai yiwu ba, da fara wannan aikin a debo malami da dalibansa sama da dari biyu ba,da kadan-kadan ne za a fara har a kawar da almajiran gaba daya don wannan makarantar tana daukar yaro dubu, amma kasan za a bi a hankali ne saboda shirin ya cimma nasara.  

Sa’annan mu a wannan makaranta ba mu da wata matsala, na tabbata uwayen yaran da aka kawo za su yi alfahari da wannan makaranta bayan hutu. Kuma ya dace malamai su kawar da tunanin ana son akashe makarantun zaure ne ta wannan hanya. A karshe in sanar da al’umma ba a daukar kowane yaro sai almajiri idan aka bada dammar daukar dalibai daga wajen gwamnati.

A ziyarar da Aminiya ta kai  a makarantar domin ganin ko kudirin  da aka kafa makaratar kansa ya cimma nasara a zagayen da wakilinmu ya yi kafin wani malami ya tsayar da shi da bukatar ya nemi izinin hukumar makaranta  ya fahimci makarantar na bukatar kulawar shugabanni, musamman a in da aka ware domin karatun allo, an cigaba da karatu a cikinta tun bayan bude ta.

Mataimakin shugaban makarantar ya ce hukumar bayar da ilmin furamare ta jiha ta hana su cewa komai sai da izininta.

Wakilinmu ya yi kokarrin zantwa da shugaban hukumar Shu’aibu Gwanda Gobir amma lamarin ya ci tura.

Kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba kan gina makarantar domin har yanzu ba a samar da wata irinta ba a jihar da kananan hukumomi, makarantar ba ta yi bunkasar da aka kudurta ba, hakan ya sanya ake zargin hukumomi a jiha basa son a yi wa manema labarai bayanin halin da makaratar ke ciki.