EFCC Ta Kama Wasu Bokaye Da Suka Damfari Dan Siyasa Miliyan 24
Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama bokaye biyu wadanda suka hada kai wurin damfarar mai neman kujerar dan majalisar wakilai a Ekiti, kudi har N24 miliyan. Kamar yadda Wilson Uwujaren, mai magana ga yawun EFCC ya fitar, hukumar tace Abiodun da Wale Adifala, tare da Ifawole Ajibola wanda aka fi sani da Baba Kalifa wanda ya tsere har yanzu ba a kama shi ba, sun shiga hannun hukumar ta jihar Legas a ranar 7 ga watan Yuli.
Hukumar tace su ukun sun hada kai wurin damfarar 'dan siyasan N24,071,000 wanda suka yi ikirarin zasu yi amfani da shi wurin bokancinsu domin cikar burinsa. Kamar yadda EFCC tace, a cikin bincikenta, Adifala ya bayyana cewa ya karba kudin wanda ya hada da N2.9 miliyan wanda yayi ikirarin zai siya bakar sanuwa, ruwan kasa da fara, raguna, turare da zobba daga cikin abubuwan da ake bukata domin aikin.
Hukumar tace Ibrahim wanda yake da alaka da 'dan siyasan ya tabbata da cewa ya karba kudade a lokutan daban-daban.
Hukumar EFCC tace sun yi kamen ne sakamakon korafin da aka aike musu da shi bayan bokayen sun karbe kudin, kuma dan siyasan ya so karbar kudinsa amma abun ya ci tura.
managarciya