Ambaliyar ruwa ta raba mutane 800 ga muhallansu a Sakkwato

Ambaliyar ruwa ta raba mutane 800 ga muhallansu a Sakkwato
Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA jami'anta sun duba hasarar da ambaliyar ta jawo karamar hukumar Silame da Binji.
Jami'an hukumar sun duba yadda ambaliyar ta yi barna a ƙananan hukumomin guda biyu dake jihar Sakkwato.
Mamakon ruwan sama da aka yi kwana biyu a satin da ya gabata sun yi wa mutane 3,850 barna a ciki sun raba 800 da muhallansu.
Ambaliyar ta shafi gonakin kusan hekta  318 a wadannan ƙananan hukumomi biyu.