Akwai 'yan fanshon da ke karɓar 4,000 a wata a Borno - NLC

Akwai 'yan fanshon da ke karɓar 4,000 a wata a Borno - NLC

Ƙungiyar 'yan kwadagon Najeriya reshen jihar Borno ta ce wasu mutanen da suka yi ritaya a jihar har yanzu ana biyansu dubu hudu a matsayin kuɗin fanshonsu a wata.

Shugaban ƙungiyar Mista Yusuf Inuwa ne ya bayyana haka yayin bayanin da ya gabatar a bikin ranar ma'aikata na 2024 wanda aka yi a jihar Borno.

Ya nemi a sake duba yadda za a kyautata kudin da ake biya domin faranta rayuwar 'yan fanshon.

"Muna miƙa ƙoƙon bararmu gabanka mai girma gwamna kan wasu 'yan fansho da har yanzu ake bai wa naira dubu hudu kowanne wata a matsayin kudin fansonsu, kuma babu shakka wadannan kudi ba za su isa ba.

"Muna roko da gwamna ya shiga wannan lamari ta yadda za a sake duba abin da ake biyansu", kamar yadda shugaban ya roƙa.