WATA UNGUWA: Fita Ta 22

WATA UNGUWA: Fita Ta 22

BABI NA ASHIRIN DA BIYU

 

 

 

Ta ɗago tare da share hawayenta ta ce"Ba fa komai 'yar'uwa."

 

Murmushi matashiyar yarinyar da ba zata gaza shekaru Ashirin da biyar ba ta jefe ta da shi sannan ta ce "Ki yi haƙuri, ba wai ina da burin na yi miki katsalandan a rayuwa ba ne, amma kin san ance _labarin zuciya a tambayi fuska,_ sannan shi kuka ai ba a yin shi sai da dalili."

 

Maheerah ta sauke ajiyar zuciya tare da kawar da kanta daga duban matashiyar.

 

"Sister ki yi haƙuri, ki bar ni haka zuciyata da gangan jikina suna buƙatar hutu."

 

Tana gama faɗa ta kifar da kanta akan cinyoyinta tana mai ci gaba da shessheƙar kuka.

 

Matashiyar ta zuba mata na mujiyarta cikin alamun tausaya ga budurwar.

 

Wani matashi mai faɗin rai dake zaune a kujerar gabansu ya juyo a hasale yana duban Maheerah cikin fusatacciyar murya ya ce

"Habah baiwar Allah! Gaskiya kina shiga haƙƙinmu, ki sani fa kowa dake nan ba ya rasa damuwar dake cin zuciyarsa amma ya jure."

 

Caraf matashiyar yarinyar ta karɓe zancen da faɗar "Allah Ya baka haƙuri bawan Allah, amma baka san damuwar dake addabar zuciyarta ba, kada ka manta kuma, hawaye ruwa ne mai tsarki da yake rage dattin damuwar dake zuciyar mutum ko da kuwa bai wanke damuwar duka ba. Me yasa kake son ƙara mata dafi fiye da dafin dake zuciyarta?"

 

"Kina da gaskiya 'yanmata, ka yi haƙuri bawan Allah nan motar haya ce dole sai an yi haƙuri, zama ne na ɗan lokaci muna sauka kowa zai kama gabansa ba kuma lallai ne mu sake haɗuwa ba a rayuwa." Wata mata dake gaba ta fara magana, sannan ta ƙarashe zancen tana duban matashin dake zaune kusa da ita.

 

A haka motar ta ci gaba da tafiya tsawon lokaci ba tare da Maheerah ta ce da kowa ƙala ba. Ko da aka tsaya cin abinci ma bata sauka ba sai matashiyar ce ta siyo mata abin taɓawa da kuɗinta, amma Mahee bata karɓa  ba, ta girgiza kai kawai ta ci gaba da zama shiru tamkar sabuwar kurma.

 

Da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare motar ta ci birki a tsakiyar tashar Babban birnin Balgori. Nan fa hayaniya ta kacame Fasinjoji suka fara sauka daga motar.

 

A tare Maheerah da matashiyar nan suka sauko daga motar, aka fara kunce kayan dake boot sauran Fasinjoji suka je ɗauko kaya yayin da Maheerah ta koma gefe ɗaya a cikin tashar ta samu guri ta rakuɓe tana ƙarewa tashar da halittun cikinta kallo.

 

Tsawon lokaci ta shafe a haka tana nazari da zancen zuci 'Yanzu ina na dosa kenan? Rayuwa a birnin da bani da kowa kuma ban san kowa ba anya hakan zai haifa mini ɗa mai ido kuwa?'

Dafa kafarɗarta da aka yi ne ya janyo ta daga duniyar tunani zuwa duniya ta zahiri. Kamar wacce ta farka daga dogon bacci ta juya a ɗan razane ta kalli wanda ya dafa ta.

 

Matashiyar nan ce ta ɗazu, don haka ta sauke nannauyar ajiyar zuciya 'Hmmm' ba ta ce komai ba.

"Sunana Sorfina Salis inkiya London girl, na fahimci kamar baki san kowa a nan garin ba da alama kuma kina cikin matsananciyar damuwa shi ya sa na kasa tafiya na bar ki, ya sunanki ne?." Ta faɗa lokacin da ta samu guri a gefen Maheerah ta zauna.

 

Murya a sanyaye Mahee  ta ce "Sunana Maheerah Isah an fi kira na da Mahee."

 

"Maheerah! Nice name." Sorfina ta faɗa sannan ta ɗora zancen da cewa "Am! Kin ga nan tasha ce, kuma yanzu dare ya yi, bai kamata mu yi magana a nan ba, idan ba damuwa ki biyo ni mu je gidana sai mu yi magana a can."

 

Kallon rashin yarda Mahee ta shiga yi mata don sai a lokacin ma ta ga yanayin shigar yarinyar da taimakon hasken ƙwayayen lantarki da suka kewaye tashar.

 Tana sanye ne da ƙananun kaya riga da wando ɗamammu sai wani matsakaicin mayafi da ta rufe kanta da kafaɗunta da shi, a kanta kitso ne na attach ta zubo gashin a gaban wuyanta, hancinta kuwa yana maƙale da dutse irin abin adon nan na 'yan bariki. 'Anyah zan yarda da wannan kuwa ko dai...'

 

Tana cikin zancen zucin ne ta tsinto muryar Sorfina tana cewa "Ki yarda da ni ba zan cutar dake ba, zan so dai ki bini ne saboda ki samu nutsuwa, amma ba zan miki dole ba."

 

Tana gama faɗa ta miƙe ta yi gaba, ba tare da wani tunani ba Mahee ta miƙe cikin hanzari ta bi bayanta.

 

Ta ce "Sister zan biki, na yarda dake."

 

Sorfina ta yi ƙayataccen murmushi sannan ta ja hannun Maheerah suka ƙarasa gaban wata dalleliyar mota da ba ta jima da yin parking ba suka shige, motar ta hau titi cikin sauri.

 

******""

 

Bayan kamar sa'a ɗaya da rabi da saukar su Mahee tana zaune a ƙawataccen falon da ya sha kayan alatu sanye da wata doguwar riga pink mara hannu. Lokaci zuwa lokaci tana gyara rigar tare da saka hannunta tana kare jikinta duk ta kasa samun nutsuwa, yanayin shigar bai mata ba sam. Sai ga Sorfina ta fito daga ɗaya daga cikin daƙunan gidan ta ƙaraso falon tana jifar Maheerah da murmushi sannan ta zauna kusa da ita.

 

Ta ce "Ina fatan baki da wata matsala, sannan kin ƙoshi babu sauran yunwa ko gajiya a tare dake."

Mahee ta gyaɗa kai tare da faɗar "Eh, Alhamdulillah sai dai...."

Ta kasa ƙarasa zancen.

 

"Ki saki jikinki sister, ki ɗauka cewa nan gidanku ne kuma ni yar'uwarki ce, ki faɗa mini dukkannin damuwarki da burukanki, in Allah Ya Yarda ba za su gagara ba kuma zan taimaka miki da abin da bai fi ƙarfina ba."

 

Ta ci gaba da gyara rigar jikinta tana kare jikinta da hannayenta.

 

Sorfina ta yi murmushi a ranta ta ce 'Da alama bata saba da irin wannan kayan ba.'

a zahiri kuwa cewa ta yi "ina jinki sister, ki ba ni labarinki da abin da ya rabo ki da gida."

 

A take sauran annurin dake kan fuskarta ya ɗauke lokaci ɗaya ta haɗe fuska tamkar limamiyar 'yan wuta. Can kuma sai ga hawaye sun fara wasar tsere a fuskarta.

 

"Oh god! Yi haƙuri sister, ban san tambayar zata ƙona miki rai haka ba ki yafe min." Cikin damuwa ta yi zancen.

 

Mahee ta saka tafin hannayenta ta share hawayen sannan ta sunkuyar da kanta ta ce "Sister ki yi haƙuri ba zan iya amsa miki wannan tambayar a yanzu ba, kuma bana son ki sake tambaya ta game da ni, amma ina da buruka guda biyu da nake so in cika wanda silar su ne na baro gida idan zaki taimaka mini."

 

Ta yi shiru tana sauraren amsar da Sorfina zata bata.

Cike da tausaya Sorfina ta kalle ta "ina jin ki, waɗanne buruka ne haka?"

 

Ta yi murmushin yaƙe ta ce "A'a sister ba yanzu ba dare ya yi, kuma ma na ga mijinki yana gida ki koma wurin shi kawai da safe idan ya fita za mu yi maganar In sha Allah saboda sirri ne."

 

Sorfina ta wadata fuskarta da murmushi sannan ta miƙe tana fadar "Shi kenan zo mu je na nuna miki makwancinki."

 

Ta shiga gaba Maheerah ta miƙe ta bi bayanta a ranta tana cewa 'wannan matar da alama 'yar gayu ce tana son kwalliyar ƙananun kaya masu bayyana surar jiki.'

 

A dai dai ƙofar wani ɗaki Sorfina ta ci burki sannan ta tura ƙofar ta shiga tana faɗar "Daga yanzu nan ne ɗakinki, har zuwa lokacin da kika gaji da baƙunci a gidan nan. Idan akwai abin da kike buƙata sai ki kira ni, kawo wayarki na saka miki lambata."

 

Sai a lokacin Maheerah ta tuna tana da waya ta ce "Ina jakata kuwa?"

 

Sorfina ta raɓa ta gefenta ta wuce ba tare da ta amsa mata ba, ta ɗauko jakar ta miƙa mata.

 

Maheerah ta buɗe jakar ta ɗauko wayar ta miƙa mata ta ce "Ga ta."

 

"Ita ce wayarki?" Ta faɗa lokacin da take kunna wayar, domin a kashe take gaba ɗaya.

Ta ce "Eh ita ce."

 

Lambar ta saka mata sannan ta yi mata sallama ta fita a ranta tana mamakin wannan yarinyar mai ban al'ajabi, ga ta dai kyakkyawa ajin ƙarshe amma wace ƙaddarar ce ta faɗa mata haka? Kuma me ya same ta duk jikinta a farfashe kamar dai wacce aka yi wa tsinannen duka?  A gaskiya ta ƙagu ta ji labarin Mahee, mai yiwuwa ta samu wani darasin mai amfani.

 

Washegari tun da asuba Maheerah ta farka, abinka da sabo da lokacin sallah ya yi duk nauyin baccin da ke kanta matsawar tana cikin hayyacinta to za ta farka. Don haka tana farkawa ta shiga banɗaki ta yi alwala ta tada sallah.

 

Bayan ta idar ta koma bacci, sai wuraren ƙarfe tara ta farka kasancewar jikinta duk ya yi tsami sallar ma da ƙyar ta yi, ko da yake abin ne ya haɗe mata ga gajiyar zaman mota ga kuma tsamin jikin dukan da ta sha a hannun Baba.

 

Da ƙyar ta buɗe kumburarrun idanunta waɗanda har yanzu ba su gama sacewa ba, ta yunkura da ƙyar ta tashi zaune. Sai dai me? Ta gagara saukowa daga kan gadon hannunta na dama da ƙafarta ta hagu sun kumbura sosai.

 

Rashin sanin abin yi ya saka ta kai hannu ta lalubo wayarta ta dannawa Sorfina kira.

 

Sai da ta tsinke ta sake kira sannan aka ɗaga. Murya ƙasa-ƙasa ta ce "Mahee ce, don Allah ki zo na kasa tashi."

 

A ruɗe Sorfina ta jefo mata tambaya "Me ya same ki ne Sister?"

 

"Ta runtse ido, ina ganin na ji ciwo ne a hannu da ƙaf.." bata ƙarasa zancen ba ta ji kiran ya tsinke.

 

Cikin abin da bai fi mintuna biyu ba sai ga Sorfina ta shigo ɗakin da gudu. Ta karasa gaban Mahee cikin hanzari "Sannu Sister zo na kama ki mu fita falo."

 

Ta kama Maheerah tare da saƙala hannunta a wuyanta suna takawa a hankali har suka ƙaraso falon ta ajiye ta akan doguwar kujera sannan ta nufi ɗakinta da hanzari.

 

Bayan ficewarta daga falon ne Maheerah ta ji  a jikinta kamar dai ana kallon ta. Ɗagowar ta ke da wuya, ta haɗa ido da matashin da take kyautata zaton mijin Sorfina ne, yana zaune a dinning table ya kafe ta da ido ko ƙyaftawa ba ya yi, tamkar jikan mayu.

 

Nan take ta ji ta tsargu sai ta sunkuyar da kanta ƙasa, cikin tsananin jin kunya, ga shi ko hijab babu a jikinta doguwar rigar jiyan ce a jikinta sai hula, rigar kuwa ta kamata sosai, ko Sorfina dake mace ta ji kunyar ganinta da ta yi sanye da rigar kasancewar a baya bata taɓa shiga makamanciyar wannan ba. Ko gurin Jafsee da take zuwa suna hutawa ai da uniform ne.

 

Bayan 'yan daƙiƙu sai ga Sorfina ta shigo falon cikin hanzari hannunta riƙe da magani pain reliever ta taka zuwa gaban matashin sannan ta ce "Lovely don Allah taimaka ka zuba mini ruwa a cup na bata magani."

 

Bai ce komai ba sai murmushi da ya yi ya tsiyaya ruwan ya miƙa mata, ita kuma ta kaiwa Maheerah tare da ɓalla mata maganin ta sha.

 

"Sannu Sister, bari a kira likita ya duba ki."

 

Ta juya ta koma gaban farin matashin ta ce "Lovely  ka kira mana likitanka ya duba ta please."

 

"Yadda kika ce gimbiya." Abin da ya faɗa kenan sannan ya ɗauki wayar shi ya miƙe yana faɗar "Ni zan fita, zan kira shi yanzun nan."

 

"Take care of yourself bye." Ta faɗa cikin sarrafa harshe da karairaya sannan ta raka shi ta dawo gun Mahee.

 

"Sannu Sister, yanzu zaki ga likitan ya zo."

 

"Ai ma na fara jin alamun sauƙi kada ki damu."

 

Ta ɗan muskuta sannan ta ce "Yanzu zan faɗa miki burina..."

 

"Ki bari ki sami sauki Sis." Sorfina ta katse ta.

 

"Ka da ki damu, jikina ne ke ciwo ba wai bakina ba, baki kuwa shi ke magana. Yanzu ne kaɗai damar da zamu iya yin magana a tsanake tun;da maigidan naki ya fita."

 

Sorfina ta yi murmushi mai ma'anoni sannan ta ce sannan ta ce "Ina jinki."

 

"Burina na farko shi ne ina son na faɗa harkar bariki sannan na goge kuma na yi ƙaurin suna a cikinta."

 

Cikin hanzari Sorfina ta ɗago kai tare da zaro ido ta ce "Me nene?"

 

Murmusawa Mahee ta yi "Yi haƙuri yar'uwa na san zaki ji abin wani banbarakwai wai namiji da suna Zainabu, amma ba shakka wannan shi ne burina na farko, sauran burukan zan faɗa miki idan lokaci ya yi."

 

Sorfina ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan ta matsa kusa da Mahee tare da kama hannunta ta ce "Na ji sister, kuma kamar yadda na miki alƙawari zan taimake ki, amma ki sani tun lokacin dana ɗora idona a kanki Allah Ya ɗora mini sonki, ina jinki kamar ƙanwata ta jini don haka zan ba ki shawara, ki haƙura da wannan burin naki domin ba zai haifa miki ɗa mai ido ba."

 

Maheerah ta janye hannunta daga cikin na Sorfina sannan ta kawar da kai gefe ta ce "Me ya saka kike son na janye burina da baki san dalilin kafuwarsa a zuciyata ba?"

 

"Saboda Barikanci ba sana'ar kirki ba ce, kuma ba a tsintar wata riba a cikinta face rasa mutunci da ƙima daga ƙarshe kuma takan jefa mai yinta cikin kogin nadama da ba zai taɓa iya fita a cikinsa ba har abada. Na san bariki ciki da bai domin ita ce silar rasa komai nawa a rayuwa."

Duk da cewa zancen Sorfina na ƙarshe ya jefa ta a ruɗani har ta kasa banbamta ɗaya da biyu, amma yana da kyau ta mayad da hankalinta akan burin da ya fantsamo da ita a duniya kuma ta bashi muhimmanci, don haka ta sake tamke fuska sosai ta ce "Na gode da shawararki sister, amma ba zan iya tumɓuke wannan buri nawa ba. Idan ba zaki taimake ni ba ya kamata na sani tun wuri don na san inda dare zai yi mini."

 Ummu inteesar ce