ANA BARIN HALAL...: Fita Ta 14

ANA BARIN HALAL...: Fita Ta 14

ANA BARIN HALAL...

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* '

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

*PAGE* 14
Haɗuwa iya haɗuwa wurin programm ɗin Aunty Jeedah yayi kyau, don komai akace da ƴan boko babu bakin magana, hidima iya hidima anyi shi, gayu iya gayu mun ganshi, Aunty jeedah ƴar'gayu ce mai amsa sunan gayu na na'am, kuma ita ma babu laifi kyakkyawace ajin farko, amma dai bata kai Aunty Bintu ba, sai dai ta nunawa Aunty bintu gayu, duk da Aunty bintu babu wasa, sai dai ita Aunty jeeddah irin first class ƴan gayun nan ne, nidai farin ciki nakeji ganin matan yayu na duk babu na zubarwa, a zuciyana addu'a nake Allah yasa itama ta zama mai kirki irin Aunty bintu, domin Aunty bintu irin matan nan ne da samun su a cikin al'ummah sai an sha wahala, zuciyarta mai kyau ne, gashi suna zaune lpy da yayah mohd.
Muryan DJ ne ya karaɗe wurin da neman dangin ango, haka muka taso da ƴan'uwan ummie, Abbah da mu ƴan gidan mu muka shiga filli, Aunty bintu
Aunty Rakiya, Adda, Aunty asma'u, da wata ƴar ƙanwar maman mu Aunty halima suka taso a manya suka fara mana liƙin kuɗi na gasken gaske, kowa ka gani kwance bounch kawai takeyi tana liƙi, ganin hafsy nayi tana liƙi da ƴan 100 ɗinta, sai lokacin na tuna danawa, haka muka shiga liƙawa juna cike da farin ciki,  daga nan kowa taje ta zauna.
Bayan ƙawayen amarya sun chashe sai DJ ya sake fito da amaryah tsakiyan fili, gayyatan ƴan'uwan ango yayi fili ds muzu mu fanshi amaryan mu, nan ma amaryah taga ruwan liƙi da muka fito muka mata, nidai ban ankara ba sai dana ƙarar da kuɗin jakana, kuma da na barshi hadda na wurin dinner na ajiye, saboda naji Ali jita zaizo, duk ɗaga idon da zanyi sai mun haɗa ido da amaryan mu, muna haɗa ido take aiko mun da murmushi, nima sai na mayar mata, Aunty Bintu na riƙe da hannunta suna rawa, Aunty Rakiya sai liƙa musu kuɗi sukeyi, gaskiya luyafan ya mun daɗi, sai bayan ishaa muka bar wurin, mun dawo gida bamu daɗe ba Aunty bintu ta kwashe mu duka har dasu ummitah da maryam mukayi gidan ta, dole sai driver ne ya ɗauko wasu, saboda akwai ƴan mata biyu da suka ƙaru ɗaya  ƴar gidan Goggo ce ƙanwar ummi wato zainab, sai kuma hadiza ƴar ƙanin baban mu ne daga tafawa ɓalewa tazo, hadiza tana B.U.K tana karanta Accounting, itama ƴar gayu ne sosai, ga rawan kai, amma kuma tana da kirki da son zumunci,  idan munje garinmu a ɗakin mamanta muke sauƙa, zainab kuma ƴar Goggo tana kashere, chan Gombe state, zainab bata cika son mutane ba kuma bata cika yawan magana ba, so ita zaiyi wuya ma ka ganta cikin mutane saidai irin haka ya faru kaman lokacin biki, gara ma yayarta Nanah mai sunan ummin mu, ita tana da son mutane sosai, yanzu ma bata da lafiya ne da nasan komai da ita za'ayi.

Gidan Yayah mohd flat uku ne dama a ciki yanzu an gyara na yayah Ahmad inda za'a saka amaryar shi, duk da Abujah zasu zauna amma nan za'a kawota, kai mutanen nan sun wuce reni, nan gidan ma sun jere mata shi, haka gidan dayake Abujan ma an jere shi, gidan dayake farkon shigowa shine aka barwa Yayah umar, na tsakiya kuma yayah mohd, wanda yake ƙarshe shine na yayah Ahmad, mun shigo bamu daɗe ba yayah Ahmad da yayah mohd suka shigo gidan, a parlor suka zauna suna hira, Aunty bintu macece mai himman gaske, gata da iya kula da miji, abun ya ban mamaki da naga ashe sai da tayi abinci tukun ta fita, haka ta haɗa abincin ta saka hafsy da ummita suka wuce da shi dinning wasu yayah, gidan kana shiga parlorn yayah ne da dinning section sai ɗakin shi toilet a ciki, sai kuma guest room a parlon shima haɗe da toilet, sai kabi wani ɗan corido da zai shigar da kai wani ɗan madaidaicin parlor mai ɗauke da ɗakuna biyu, shima ko wanne da toilet a ciki, shine side ɗin Aunty bintu, kuma ko wani side haka yake, gidan babu laifi yayi kyau sosai,ballantana da tasamu kayan kece raini.
Parlon muka shigo dukkan mu muka gaishe su, Yayah mohd na zolayan hadiza akan sunyi waya da bappanmu wai yayi mata cikiyan miji a birni ta bar ƙauye, da yake bakinta baya shiru haka ta dinga maida mishi amsan da ae shi tazaɓa, saboda haka ya bawa bappah amsan ta samu wuri, idan kuma bashi iyawa ga yayah Ahmad, shidai yayah Ahmad murmushi kawai yakeyi, haka tayi ta zolayan su shida yayah Ahmad, amma yayah mohd kaɗai ke maida mata amsa Aunty bintu na taya shi, yayah Ahmad dai sai murmushi yake yi baya iya cewa komai, ko ta tsokano shi sai dai yace ta jira Jeeddah shi tafi ƙarfin shi, zainab dai sai kallo ta ke binsu da shi kaman ba abokan wasanta ba, bayan sun gama chakalan junan su sai suka koma ciki, Aunty bintu kawai aka bari a wurin sai ni da naje kusa da yayah mohd na zauna, hannun shi na riƙo ina dariya, shima dariyan ya fara yana, "akwai abunda bestyn yayah moh takeda buƙata kenan, dariya na sakeyi ina ƙara riƙo hannun shi, "yayah duk duniya kaida ummie kuna saurin ganoni, narasa sanin dalili", na faɗa ina dariya, Aunty bintu ne ta bani amsa itama tana dariyan mu, "saboda duk duniya sun fi kowa sonki, shiyasa kowani language naki suke ganewa", ɗago ido yayah Ahmaɗ yayi yana dubanta, kaman baxai buɗe baki ba, amma sai naga kaman bashi ba yace, "banda son kai matar yayah, nasu ne ya bayyana, amma ni son da nakeyiwa Ayshaa sai inaga kaman yafi son da uwa takeyiwa ɗanta, saboda ko jeeddah ta gane, idan nayi fushi tou hiran Ayshaa take mun na sauƙo, duk abunda yake saka ni farin ciki kawai na ganta tana annashuwa", ya faɗa yana maida kallon shi kaina, da sauri na sake hannun yayah mohd na koma jikin yayah Ahmad na kwantar da kaina a kafaɗan shi, a hankali nace yayah Ahmad baka taɓa gaya mun ba, sai dai abunda kullum nake tunani a raina shin acikin ku ni waya fi nuna mun so da kulawa ne? Sai na ga kowa yana sona, kaga yayah mohd na shaƙu da shi kuma bana iya ɓoye mishi komai na, kuma sai inaga shine yake bani solution na kowani  abu da ya sha mun kai, kuma yana son farin cikina, kai kuma Yayah Ahmad kasan me nakeji akanka?" girgiza kai yayi alaman bai sani ba, riƙo hannun shi nayi nace, "duka rauni na yana kanka, haka kawai zuciyata take jin tausayinka ko shiru kayi sai na dinga jin babu daɗi, kuma duk ranan da kazo sai naji tou gidan ya cika, duk abun da yayi giɓi a gidan ya cika,"
"ni kuma duk wanda naga zai tayar miki hankali ko zai taɓaki sai na rushe duniyar shi gaba ɗaya, duk wanda ya taɓa mun ke zan tada ƙaramar yaƙin ƙare dangin shi duka", yayah umar ya faɗa yana shigowa cikin parlon shida hussainin shi yayah ishaq, dariya dukkan mu parlon muka kwashe da shi, da gudu naje na rungume shi ina dariya, "yayah umar nasan kana sona, ni ma ina sonka, amma kai kana mun tsawa wataran har sai nace kodai ba yayah umar ɗina bane" dariya yayi yana riƙe dani muka zauna, " bazaki gane bane Ayshaata, ina miki faɗa wataran don wancan autar ummi marar jin maganan, laifinta ne yawanci yake shafanta, amma daga Abba, Ummi, yayah mohd, yayah Ahmad, fitinanniyar ɗakin mu, duk babu wanda yakaini sonki", ya faɗa yana duban yayah ishaq da yake binshi da harara, shi kuma yayah umar yana mishi dariyar mugunta.
Shigowar hafsy da zunɓurarren baki a gaba ya sake bawa kowa dake parlon dariya, gefen Aunty bintu taje ta rakuɓe tana turo baki gaba tace, "Adda duk wannan son da suke faɗa miki suna miki duk abakine, ni nawa bazai faɗuba, ni nawa da nake miki baxai misaltu ba, har abada har gaban abadah baxan so abu kwatankwacin irin kiba a duniya, ni ko ummi da Abba bana jin ina da kusanci dasu sama da ke, ko ƴaƴan da zan haifa suyi haƙuri su biyo bayanki Adda, ballantana kuma miji, sorry ɗinshi" ta ƙarasa tana hararan yayah ishaq, murmushi yayi ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana danne-danne a jikin wayan shi.
Gaba ɗaya hira muka kachame da shi, kaman ba jiran yayah Ahmad abokanshi sukeyi ba, sai da yaga wayan su yayi yawa tukun ya mana sallama ya tashi zaifita, lokacinne yayah mohd yake tambaya na meye nake so? "kuɗin liƙi yayah zaka ƙara mun, nawa duk na ƙarar a wurin event ɗin yau, gashi akwai dinner".
Ɗan dawowa da baya yayah Ahmad yayi yace, "ki bar yayah moha, goben kituna mun na baki ko", godiya nafara mishi bai saurare ni ba yayi waje, harara na hafsy tayi," wallahi Adda duk kuɗin da aka baki sai mun raba, wannan ae wayo ne, sai ki lallaɓa kowa komai sai ke, tou ni ɗin da babu mai sona sai an bani",  dariyar ta kowa yakeyi, Aunty bintu tace kada kiji komai ke baga ishaq ba ae kece favourite sister shi, kema kina da wanda ya damu dake over, kuma gani nan nima ke nafi so", 
Turo baki hafsy ra sakeyi tace, "haba Aunty bintu nafasan gaskiya, Adda kema kika fi so, ina jinki fa ranan kikace Adda duk tafi mu kyau saboda tana kama da mijinki, wai har baki gajjiya da kallonta, wato nice mummunar wanda ake gajjiya da kallona? Daɗinta ma da Abba da Aunty Rakiya nake kama, kuma ina isar musu da saƙo za'a samu matsala da kowa, ni yanzu bandamu da ku soni ba bari na jira zuwan matar yayah Ahmad, naga ko ni zata kama? Idan kuma takama mai ƙwala-ƙwalan idon nan sai najira ta yayah umar da haƙuri, don ita kam nasan nice overoll" ta faɗa tana kallon yayah umar tana dariyan shaƙiyanci, dariya dukkan mu mukeyi, shidai yayah ishaq hararanta yake tayi, wanda narasa na menene, "
Haka mukai ta hira har saida yayah mohd ya bar parlon, yana tafiya Aunty bintu ta wuce kitchen, kallo na yayah ishaq yayi yace, "tou ae sai ki tashi ki koma ciki mai masoya da yawa, amma nidai ki sani favourite ɗina hafsy ce, duk da ma yanzu ta gama yaɓa mini baƙaƙen magana, wai nine na ƙarshe acikin wanda zata so, hala har da wannan ƙaton banzan yayantan", ya faɗa yana kai naushi wa yayah umar, nidai banbi takansu ba saboda nagane inda zance ya dosa, kawai miƙewa nayi nayi hanyan ɗakin Aunty bintu, ina kusa da shiga naji yayah umar yana ƴar'uwa ki turo mun ummitah plz, mirmushi kawai nayi na wuce ciki, babu daɗewa kowa ummitah ta fito parlon, kafin nan kuma yayah umar ya koma kan dinning yana jiranta, ina shiga ɗakin na kalli su maryam nace, "gara fah muma muyi takanmu mu samu abokanan rayuwa, don idan muka zauna ta boko tou zamu raka ummitah da hafsy ɗakin aure".
Wani fari da ido hadiza tayi tana wani juya jiki tace, "ke kenan da kika zauna zaman jira, ni dai akwai wani ɗan unguwan mu suraj, yana aiki yanzu da NNPC, shima yace mun yasan Yayah mohd suna tare a lagos amma yayah seniour shine, tou nidai zanyi wuff da shi, don insha Allah shekaran nan da zamu shiga zasu zo suyi gaisuwa", ta faɗa tana wani jujjuya jiki tana saka kayan baccin ta, kallonta kawai nayi ina dariya, na juya kan zainab nace ƴar'uwa kefa?
Harara ta mun tace, "sai kin samo na karɓa irin na habiba," dariya muka kwashe da shi, na juyawa wurin fatima nace,"kefa sis",
Itama dariyan tayi tace, "ni yanzu akwai wanda ya mun magana, amma baya ƙasan yana masters a London, yayan ƙawata ce, sunan shi kabir ɗan maiduguri ne shuwa ne shima, sai kumun addu'a Allah ya dawo da shi lpy," tafi dukkan mukayi muna mata guɗa, kallon maryam nayi nace "besty yyh ke kuma ina muka dosa"? Murmushi tayi tace nidai besty gamu nan muna addu'a, ina ga wannan lokacin sai mundage kada yaran nan su bamu kunya, don naga har ƴan aika muka zama musu, ni ae bansan yayah umar me yake tafiya ba, jiya fah aikana yayi na ƙirata", dariya muka kwashe da shi nace nima baka shi yanzu ya aiko ni ba, kawai besty muma mu dage mu samu wanda zamuyi wuff da shi.
Muna gamawa muka fara tsara yadda zamu kwanta, nan ɗakin Aunty bintu akwai wani lazychair a ciki, kai na hau na kwanta, gadon kuma hadiza, maryam da zainab zasu kwanta, ɗayan ɗakin da yake gefe inda fatima suke sauƙa tace zasu kwanta ita da hafsy da ummitah, haka mukayi sallama kowa ta kama wurin kwanciyarta, ina rufe ido sai tunanin fararen nan ya faɗo mun a zuciyata, da sauri na buɗe ido na, ganin an kashe wuta sai na mayar da idon na rufe.


*AUNTY NICE*