ANA BARIN HALAL...: Fita Ta 23
ANA BARIN HALAL...
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 23
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
**********
Koda muka isa gida kowa haraman sallah ya fara, muna idar wa fatima ta juyo tana kallo na, batace komai ba sai ido da ta zuba mun, gajjiya nayi da kallon nace, "wannan irin kallon fah teemah"?
Murmushi tayi ta ce, "naga alaman M.G yagama tsaraki kin tsaru yau, don naga sai wani annuri ne ke fita a fuskar ki,"
Nima murmushin nayi na girgiza kai na, "wallahi babu wani tsari teemah, kawai labarin rayuwa mukeyi, amma ba abun da kike tunani bane ya faru", ina gama faɗan haka na miƙe tsaye ina naɗe hijab ɗina, bana son mucigaba da zancen don banyi niyyan sanar da kowa yadda mukayi da M.G ba, don wannan sirrin shi ne kuma bai gama gaya mun ba, sannan bansan maƙasudin zaman namu ba ballantana har na fara isarwa wani, sai na chanja topic ɗin maganan da, "teemah kunyi waya da maryam ne yau da muka fita?" "eh ta ƙirani wai wayanki akashe, sannan hadiza ma ta ƙira" muna cikin maganan hafsy ta shigo, wani kallo ta ke mun na alaman gulma na muntsininta, bana so ta sake jawo wani magana sai na yi hanyan fita na bar ɗakin, parlor naje gefen Aunty na zauna kusa da ita, kallo na tayi tana murmushi tace, "ƴan matan ummie yyh akayi?" murmushi nayi na kalleta nace wai wannan abokin yayah Ahmad ɗinnan ne wai na dafa mishi tea, ni kuma wallahi maganan su teemah da hafsy ne bana so, don Allah Aunty kice wa ke zan dafa".
Dariya ta ɗanyi kaɗan tace, "babu komai bestyn husby na, bari su fito sai nace ki dafa mun tea ki kuma zubawa jeeddah a flask, kinga sai ki ɗauka kaman zaki kai mata sai ki kai mishi, amma yyh ake ciki akwai wani update ne"?
Murmushi nayi na girgiza kaina nace, "Aunty babu komai fah wallahi, ni bamu cika wani shiri bama da shi, kinsan baida lafiya yana da asthma, inaga shiyasa yake son shan tea ɗin", ina rufe baki su teemah suna fitowa, basu wuce minti biyar ba Aunty ta umurceni da na dafa mata tea, idan nagama kuma na zubawa Aunty J, yadda dai muka tsara, haka na tashi naje na haɗa na dafa shi tsaf sai ƙamshin kayan haɗin su na ƴan maiduguri yakeyi, sannan na haɗa sandwich, M.G kaman yasan nagama abunda nakeyi sai ga call ɗinshi, ina ɗauka yace gasu nan a parlon yayah Ahmaɗ shi da A.G.
Ajiye musu basket ɗin tea ɗin nayi akan center table ɗin da yake gaban M.G, Kallo na yayah Ahmad yayi yace ki zubuwa A.G shine zai sha, fatan dai kin saka kayan yaji ko? Ɗaga kai kawai nayi batare da na buɗe baki na amsa ba, har gaban A.G ɗin naje na durƙusa na ɗauki cup na zuba mishi sannan nasaka sandwich ɗin a kan wani plet, na miƙa mishi, kallo na yayi fuskan shi ta nuna alaman yana shan wahala, don har wani ja tayi ta kan hancin shi, murya ƙasa-ƙasa naji yace, "ki ƙara mun sugar" kallo na sake binshi da shi "na saka sugar fah sosai, taɓa kaji", eyyh kallon yau babu masifa da harara a ciki, sai mai da kanshi yayi ya kwantar ya lumshe ido, nidai ina kallon shi da cup a riƙe a hannu na, sai naga kaman numfashin yana jan shi a hankali a ƙasan ƙirjin shi, duk sai naji ya bani tausayi, murya ƙasa - ƙasa wanda babu wanda zaiji sai shi nace, Yayah A.G sannu, ka tashi kasha tea ɗin kada yayi sanyi",
Buɗe ido yayi a hankali ya ƙura mun sannan yace, "nace ki ƙara mun sugar kinƙi, bazan iya sha babu sugar sosai ba", da sauri na ajiye cup ɗin na ƙara zuba spoon ɗaya, bayan na gauraya shi na miƙa mishi, hannu ya saka ya karɓa, ina kallon shi daya kurɓa ya ɗan runtse idon shi, a hankali yake shan tea ɗin, cike da tausayi na miƙa mishi bread ɗin, babu musu ya saka hannu ya karɓa, shima a hankali ya ke gutsura, abun mamaki naga yaci har biyu, sannan ya shanye tea ɗin, rufe ido shi ya sakeyi yayi shiru, naga shirun yayi yawa gasu yayah Ahmad suna zaune akan dinning shi da M.G suna cin abinci suna ɗan taɓa hiran su, sai na miƙe zan tafi chan side ɗin yayah muhammad kawai sai naji muryan shi yace, "ki ɓalla mun maganin nan nasha plz", juyowa nayi na kalle shi, amma har lokacin idon shi a lumshe yake, tsayawa nayi shiru kaman bazan ce komai ba, sai kuma na ƙarasa inda yake na sake durƙusawa daidai inda gwaiwan shi suke na miƙa hannu na karɓi satchet ɗin maganin da yake miƙo mun, dubawa nayi naga guda ɗaya zan ɓalla na bashi, cike da mamakin shi wato ɓalla maganin ma bayajin iyawa, ko kuma samun wuri ne oho, haka dai na ɓalle mishi na buɗe baki nace "gashi", ɗagowa yayi idon shi duk sunyi kalan tausayi, hannu ya saka ya karɓi maganin, idon shi na kaina yace "ruwan ma sai nayi tambaya"? Juyawa nayi na ɗauko goran ruwan da nasan Aunty j ne ta kawo musu da drinks ɗin, zuba mishi nayi a cup na miƙa mishi, idon shi yana kaina ya saka hannu ya karɓa, bayan ya shanye ya sake yin shiru, ni kuma ganin yayi shiru ya saka na sake niyyan miƙewa don na tafi, "ban sallameki ba tukun madam" ya faɗa yana ƙura mun idon shi.
Turo baki nayi gaba alaman na gajji,
"gobe insha Allah by 9:00pm tafiya na school, akwai wani abu da kike so?"
Da sauri na ɗago kaina na dube shi, bansan yayah akayi ba naji bakina yana furta, " gobe kuma? Wani irin school kuma? Tafiya zakayi kabar Yayah M.G shi kaɗai?".
Ido ya ɗan ƙura mun kaman mai nazarin wani abu, chan kuma sai ya ɗaga kai ya dubi M.G na wani lokaci sai ya dawo da kallon shi kaina, duk yanayin shi sai naga ya canja, wannan ɗaurewa da masifan sai naga kaman babu su a yau, "M.G ne kawai damuwan ki? Baki tunanin ni yayah zan kasance? M.G kawai kike tsoron ya shiga wani yanayi bani ba ko?" ƙasa yayi da fuskan shi har dab da fuskana, a hankali naji ya furta, "ke baki da damuwa da tafiyan da zanyi ko? Zan daɗe fah, amma duk bai dameki ba sai M.G ne damuwanki ko"?.
Yana gama faɗin hakan ya miƙe tsaye bai sake duba na ba ya wuce direct hanyan waje, da sauri naga su yaya Ahmad sun miƙe suna tambayan shi jikin ne? Girgiza kai yayi alaman a'a ya fice a parlon, sallama M.G ya mun ya bi bayan shi, shima yayah Ahmad yabi bayan su, ajiyan zuciya nayi jikina duk yayi sanyi, tou ni mai nace mishi wanda baiyi dai-dai ba? Duk sai naji hankali na yayi mummunan tashi, ga wani yankewa da naji zuciyana yayi, haka na daure naja ƙafana na koma wurin su Aunty B.
Lokacin da na shimfiɗa kafaɗa na a gado sai na neme bacci na rasa, ina jin fatima da hafsy suka gama wayoyinsu suka kwanta, amma ni nakasa bacci, kuma ba komai bane ya hanani bacci sai yanayin da A.G ya fita a ɗazu, narasa tausayin shi nakeji ko me? Ko ganin baida lafiya amma kuma zaiyi tafiyan a haka makeji oho, ko kuma barin M.G da damuwan da M.G zai samu kanshi ne nake ji oho, nidai ranan ban samu nayi bacci ba har wurin sallan Asubah, saboda haka muna idar da sallah nace musu kaina yana ciwo, haka suka rabu dani na koma nayi bacci, ban tashi ba sai wuraren ƙarfe shabiyu na rana, ina tashi wanka na shiga sannan na fito parlor na gaida Aunty B, nan na samu suna ta kiciniyan haɗa girki domin 2:00 yayah muhammad zai iso, sai wani shirye-shirye Aunty B takeyi kaman wani tafiyan shekara guda yayi, duk an share gidan an baɗa mana ƙamshin su na borno, hattah Areefh yasha gayu, a lokacin hafsy ta matsu kusa dani tace , "Adda yau fa zuwan su yaya M.G biyu gidan nan neman ki, ya ƙira wayan ki akashe," kallon ta nayi nace, "shine baki tashe ni ba hafsy? Shi kaɗai ko su biyu"?
"su biyu suka zo Adda, ae yace na tashe ki a zuwan su na biyu, sai kuma ɗayan ɗan'uwan shin yace a barki tunda nace kanki ne yake ciwo, amma yace ki ƙira shi idan kin tashi", tana gama gaya mun yadda sukayi na juya na koma ɗaki domin kunna wayana, haka kawai naji ina so nasan yayah suke, kuma lafiya suka zo har sau biyu nema na?.
Ina kunnawa wayan maryam na shigowa, raina a ɗan jagule na ɗauki wayan, "besty meye haka ne, tun jiya nake ƙiranki wayan ki akashe, sannan nace ki ƙirani shima shiru, monday fah zamu koma school kunje kun rashe, baza ku dawo bane kam?" ta faɗa ba tare da jiran mun gaisa ba, ajiyan zuciya na sauƙe domin ganin wayan M.G da yake shigo mun, "besty yi haƙuri bari na ɗauki waya don Allah", katse wayanta nayi na ɗauki wayan M.G.
"Ayshaa wa kika samu haka?" gaishe shi nafara ba tare da na bashi amsan tambayan shi ba, shima bai bi takan tambayan da yayi mun ba, kawai ya shiga tambaya na yayah jikina? "da sauƙi" na bashi amsa, "Ayshaa munzo sau biyu kina bacci, dama A.G zai miki sallama ne, kin san da tafiyan shi a nan abuja ne, sai ga shi kuma ya koma ta lagos, kuma flith ɗin shi 1:00 ne, so yanzu ma muna hanyan airpot," "ina yayah A.Gn"? Kawai nasamu kaina da tambayan shi, bai jira me zance ba kawai ya miƙawa A.G wayan, baice mun uffan ba da ya karɓi wayan, amma dai nasan ya karɓi phone ɗin, saboda yadda nake jin fitan numfashin shi wanda bai daidai tu ba har yanzu, nima shirun nayi bance uffan ba, har zuwa wani lokaci sai naji yace, "yayah akayi"? Ajiyan zuciya na sauƙe da ƙarfi sannan nace, "yayah numfashinka", shiru na sakeyi, shima yayi shirun na ɗan wani lokaci, kafin chan yace, "shine damuwan ki?"
"a'a ni bashi bane",
"meye tou"?
Sai da naja lokaci mai ɗan yawa kafin nace, "Allah ya kiyaye hanya, ka kula don Allah",
"Hmmm" kawai yace sannan ya miƙawa M.G wayan, sallama M.G yamun akan sun iso zasu shiga ciki, idan ya dawo zai neme ni, mukayi sallama na kashe wayan, tagumi nayi da dukkan hannu na biyu, ban ankara ba sai naji dariyan hafsy, juyowa nayi da sauri na kalle ta, ashe tana zaune akan gado ta ƙura mun ido, tambayanta nayi yaushe ta shigo, tana dariya tace mun tun lokacin da nake soyayyah ta shigo, lokacin idona a rufe ban sani ba, hararanta nayi na fice a ɗakin.
*AUNTY NICE*
managarciya