Lissafin Ƙaddara: Fita Ta...

ana kwana ana tashi biki ya matso gadan-gadan ana ta hidindimu ƴan uwa na nesa da na kusa duk sun fara shirin zuwa biki ƴan saudiya kuwa yau Allah yayi musu sauka yau a filin sauka da tashin jirage na Aminu Kano Abban Hammad da kanshi yaje ya ɗaukosu domin shi yakeso ya fara arba da su,

Lissafin Ƙaddara: Fita Ta...

*LISSAFIN ƘADDARA*


              Na
*Zainab Sulaiman*
        (Autar Baba)


Not edited 


*DEDICATED TO SHAMSIYYA USMAN MANGA*

*MANAZARTA  WRITERS ASSOCIATION*

Kai kawai Baba ya kaɗa yabar ɗakin jiyar su Hammad sukayi masa sallama bayan Abdallah ya sanar masa da ya yafe masa kuma ya ɗau nauyin jinyarsa har ya warke sannan zai sama masa mai kula dashi tunda yasan ba mai kula dashiɗin,matarsa tana farfaɗowa daga doguwar suman da tayi bayan jibgar da tasha a wurin abokan faɗan ɗanta tace ya sallameta dan tabar zama dashi har abada sannan tayi ikirarin bakomai a aurensa sai masifa da jaraba ta kara da ba abunda ta samu a aurensa sai ci bayama da tayi gashi yayi sanadiyar lalacewar ƴaƴanta ta hanyar sangartasu da yayi,take yanke itama ya bata sallama,

haka su Ameenatuh suka goma gida ga abun farin ciki amma sai ya zaman ya koma baƙin ciki,

ana kwana ana tashi biki ya matso gadan-gadan ana ta hidindimu ƴan uwa na nesa da na kusa duk sun fara shirin zuwa biki ƴan saudiya kuwa yau Allah yayi musu sauka yau a filin sauka da tashin jirage na Aminu Kano Abban Hammad da kanshi yaje ya ɗaukosu domin shi yakeso ya fara arba da su,


Su uku ne suka sauko daga matakalar jirgin daya na bin daya har suka sauko,

cikin murna da farin ciki Abban Hammad ya tare su haɗi da rungume Al'ameen haɗi da miƙawa Baban Al'ameen hannu kafun shima ya rungumoshi,ya ɗago yana ƙare musu kallo,harar da Mami tayi mishi ne tasa yasa ƴar dariya itama ya rungumeta yana ɗan sosa ƙeya yace"kinsan nayi missin brother  duk idona ya makance"ranƙwashi takai masa tana cewa "amma ai bai makance akan ubanka ba sai akan gyatumarka"dariya suka sa su duka sannan ya karɓi akwatin hannunta sukayi gaba,

a hanya ne yake sanar dasu mutuwar auren Maryam bayan hira tayi hira,sosai sukayi farin ciki da hakan dan kuwa ko ba komai ƴarsu ce,


tuwon girma miyarsa nama domin kuwa sun samu tarbar girma daga wajen Baba da iyalinsa ko dan dukansu ƴan uwa ne dan kuwa dukansu ahaline na Alhaji Adamu(Balan gano)yan asalin kano cikin garin gano gidan karofi da ke unguwar karofi ne,

Biki yayi biki a halin gano sun bayyana yayin da tsiraru daga ahalin Abbansu Ameenatuh ma suka bayyana,


Yau take lahadi kuma yau take daurin auren Ameenatuh da Abdallah,

Shelar maroƙace ta fara bayyana yayin da suke shailanta daurin auren,
"an dauran Abdallah Yahya tare da zankaɗeɗiyar amaryarsa Ameenatuh Kamalu Kabiru Makama akan sadaki dubu dari biyu lakadan ba ajalan ba!"bayan sanarwar da mintunan da basu gaza uku ba marokin ya ƙara shelanta ɗaurin auren"ƴan gidan arziki irin albarka waanda aka haifa tsiya na bacci aure ya ɗauru tsakanin Al'ameen Yakubu Balan gano tare da zankaɗɗiyar amaryarsa Maryam Ishaq Balan gano akan sadaki naira na gugan naira har naira dubu dari ɗaya",
gaban Abban Ameenatuh ya faɗi irin mummunan faɗuwar nan "kaicona kaico da mutum irina kaico da sakacina" yanaji yana gani ƴan tsirarun abokansa da sukazo ɗaurin auren suka ringa masa Allah ya sanya alkairi shi dai yaƙe kawai yake,

a cikin gida kuwa sosai akayi farin ciki da haka "ashe matar mutum kabarinsa Allah dai yayi Maryam matar Ameenuna ce kuma ita zata kasance matarshi ta farko,ashe shiyasa ya kiyin aure lokacinshi ne bayyi ba yanzu da yayi gashi ba zato bare tsammani anyi"mahaifiyar Al'ameen tafaɗa tana share hawayen farin ciki yau taga auren gudan ɗan nata,

Ameenatuh da Khadeeja kuwa sunsha mamaki bama ya Ammeenatu dataga tsantsar nadama a idon mahaifinta taso ace Mahaifiyarta na tare da Mahaifinsu amma Allah al mudabbiru ne mai juya dare zuwa rana a fili kuma tace"Alhamdulillah"sai kuma tayi ƙasa tayi sujudu shukur,

a bangaren Umma kuwa batasan zancen auren ba sai da aka ɗaura mai makon taji baƙin cikin rashin shawartarta a matsayinta na bazawara sai ma wani irin farin ciki  da ya lulluɓeta,


masha Allah anyi biki lafiya an gama lafiya,amarya Ameenatuh an danganata da gidan mijinta dan kuwa Abbanta Mahaifinta shi da kanshi ya kaita ɗakinta sannan yayi mata nasiha sosai,


a ɓangaren Khadee kuwa tasha kuka dan hartafi amaryar ma kuka yini ɗaya duk ta rame da ƙyarma ta bari Abba ya fita da Ameenatuh dan sai da ya tsawatar mata ma,


bayan sati ɗaya da biki kowa ya watse ƴan madinatul munauwara ma sun fara shirin komawarsu bayan sun zaga dangin gidan karofi  aka wuce da amarya Maryam(Umma)kasa mai tsarki,

Zaman lafiya sosai ya wanzu a gidajen guda biyu domin Umma tuni ta baje hajar soyayyarta ta bayyanar da ita wa mijinta sai kace yara haka suke kwasar love,haka ce ta kasance a bangaren Ameenatuh duk wata kulawa da miji yake baiwa mata Abdallah bai rageta ta ko ina ba tuni ita ma ta waye tun tana noƙewa har ta faso gari take nema ma tafi ƴan gari sa nin gari,


Bayan shekara guda
Umma,Ameenatuh sai Khadeeja da take zaune jikin Umman gefe guda kuma Nana ce mahaifiyar Hammad ita da Mama ko wacce riƙe da Baby,Ameenatuh ce ta tashi ta kalli Nana tace "Momi ni dai zan koma bacci nake ji"tana faɗa tayi gaba ita ma Nana ta miƙe tana cewa" a'a jira ni mu tafi tare kar Baby ta tashi taga bakya kusa"dariya Mama tayi kafun tace "kwaji dashi ke dama Firdausi ba'a ganinki anan sai ƴar ki tana nan yanzu kuwa da kikayi jika sai kika manta da mu gaba ɗaya"itama dariya tayi ta fice tanacewa"ba haka bane wallahi Baby ce batason yawo",


tashi Mama tayi ta kalli Umma ta miƙa mata Baby dake hannuta tace"ungo bashi yasha ɗan nan akwai haƙuri bai biyo mai sunanshi ba dan babanku kwai rashin hakuri kamar zawayi"dariya sukayi su duka,

Abban Ameenatuh yayi aure ya auri wata bazawara da mijinta ya rasu shekara uku baya,

Baba kuwa ya haɗa aure Khadeeja da Hammad domin wannan itace a ƙidar jama'ar gidan karofi hada auren zumunci kuma dole kuzauna lafiya kamar yadda akayiwa su Baba,


komai ya zama tarihi sai dai a tuna na kuka ayi kuka na dariya ayi dariya  ɗiyar Ameenatuh taci sunan Khadee yaron Umma kuma yaci sunan Mahaifita(Baba)


Alhj Kml kuwa ya bawa alhj Sabo kudin auren Ameenatuh da ya biya sannan yabiya duk wani mai binshi bashi,gaba daya yanzu kasuwancin nasa baya tafiya saboda ba jari duk ya biya mutane hakkinsu dashi wani lokacin ma da kyar suke samun nacin abinci shi da matarsa,


Mijin Ameenatuh kuwa wasu ƴan kuɗaɗe masu tsoka ya ware a matsayin zakka ya bayar ta bawa mahaifinta da hannunta sannan ya gargaɗeta akan karta faɗa masa shi ya bayar kawai ta bashi a matsayin ita ta bayar,


haka ta ware rana ita da Khadee suka kaiwa mahaifinsu ziya da gwaggwaɓar kyauta mai tsoka wacce yasa yaji ɗaɗi sosai ya kumayi farin ciki tare da yi musu addu'a ya kuma nemi da su kara nemar masa gafarar mahaifiyarsu,.

Kabiru da Ahmad kuwa kanan Ameenatuh tuni akayi ram da su aka kaisu gidan dan kande su da abokansu,

Umma kuwa tana zubar da wanka mijinta ya zo ya ɗauki abarsa suka keta hazo,.

Ƙarshe

watan azumi na gabatowa to ina wa kowa barka da zuwan watan azumin Ramadan Allah yasa muganshi lafiya Allah ya ba ikon bauta masa ya kuma yafe mana albarkacin wata mai daraja ,

taku har kullum ina muku fatan alkari tare da fatan mu ƙaru da abunda muka karanta,

daga 
marubuciya 
ƴan boarding school
sajnah
auren jinsi 
 da sauransu dai 
duk wacce taci karo da ƴan boading school dan Allah a taimaka mun dashi.,
    

            AUTAR BABA CE