Bai kamata a riƙa amfani da sojoji a harkokin zaɓe ba - Jonathan 

Bai kamata a riƙa amfani da sojoji a harkokin zaɓe ba - Jonathan 

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewa bai kamata a riƙa amfani da sojoji a harkokin zabe kamar yadda ake yi a wasu kasashen duniya musamman ma Nijeriya.

VANGUARD ta rawaito cewa da ya ke jawabi a wajen kaddamar da littafai guda biyu, Jonathan, wanda shi ne Shugaban taron, ya ce, “A nan Nijeriya, mun wuce gona da iri. A yawancin sauran ƙasashe, sojoji ba sa shiga cikin gudanar da zaɓe na yau da kullum.

A cewar sa, a wasu ƙasashe, ana amfani da sojoji ne don gyaran ƙasa, inda ya kara da cewa ana amfani da Sojojin sama da na Sojojin kasa wajen ɗauka da kai dauki zuwa wurare masu haɗari.

“Amma ganin su a rumfunan zabe da kare ƙuri'u ba aikin soja ba ne. Na dawo daga Botswana watanni baya lokacin zabe. Kasa ce mai karancin jama’a, amma kusan dukkanin harkokin zaɓe da ƴansanda ake yi.

“Ayyukan da jami’an ‘yansanda ke yi shi sojoji ke yi, ciki har da tsaron hedikwatar ‘yansanda, sojoji sun karbe ragamar mulki. 

"Don haka, babban hafsan soja zai sanya jami’an soji ne kawai don su tsare kadarorin gwamnati da kayayyakin aiki," in ji Goodluck