Sarkin Kano ya halarci bikin cikar Gambia shekaru 60 da samun ƴancin kai
A jiya Litinin ne mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya isa birnin Banjul, babban birnin kasar Gambia, a wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu.
A wata sanarwa da ta fito daga masarautar Kano, ta ce ziyarar ta biyo bayan gayyatar shugaban kasar Gambia, Adama Barrow.
Sanarwar ta ce, an gayyaci Sanusi ne a matsayin babban bako na musamman a wajen bikin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai na jamhuriyar Gambia.
Ministoci da wasu jiga-jigan gwamnati da suka karbi bakuncinsa sun tarbe shi a lokacin da ya isa filin jirgin sama na birnin Banjul.
Daga bisani kuma da yammacin ranar, Sarkin ya bi sahun shugaba Barrow da uwargidan sa, Fatumatou Bah Barrow a wata liyafa da aka gudanar a wani bangare na bikin cika shekaru 60 na Gambiya.
Babban bikin ya ci gaba da gudana a yau Talata tare da fareti na musamman da sojojin kasar Gambia su ka yi a dandalin Banjul Grande.
Sanarwar ta kara da cewa ana sa ran Sarki Sanusi zai dawo gida a yau.
managarciya