MAMAYA:Labarin Soyayyar Aljani Da Mutum, Fita Ta Tara

MAMAYA:Labarin Soyayyar Aljani Da Mutum, Fita Ta Tara

 *Shafi na tara*       

 

 

Daji ne mai manyan itatuwa masu yalwar ganyayyaki wanda hakan ya tilasta ma dajin yin wani dubu mai ban tsoro .

 

Kwance take ƙasa sai barci take hankalinta kwance ga alama bata san inda kanta yake ba.

 

Wasu kattin idanuwa ne birjik a ƙasa babu kai babu jiki su kaɗai ne a ƙasa sai jujjuwa suke tamkar majaujawa, gasu jajir dasu kamar garwashi sun kewaye Huraira dake ta sheƙa barcin ta cikin natsuwa da lumana.

 

Kamar ance ta buɗe idanunta ta wagesu baki ɗaya tsammanin ta kan gadonta ne da kwanta ta sararama tsufanta itama .

 

 

Ai tana arba da waɗannan manyan kattin idanuwa zube a ƙasa birjik sai ta fasa ihu ta miƙe zaune tana kiran...

 

"Na bani na lalace ni Huraira ubanme ya kawomin idanuwa cikin ɗakina ?

Ji tai an tangare mata ƙeya ta baya ance " masifatu mu kike zagi yau kuma ? To ba shakka sai na cinye halshen naga gobe da wanda za ki yi amfani ki zagemu"

 

Da kyau ta dubi inda  take sai lokacin ta fahimci ba gidanta bane, ba ɗakinta bane cikin tsakiyar dajin Allah ta'ala take kwance ƙasan wata shirgegeiyar bishiyar kuka mai suffar ban tsoro da ban mamaki .

 

Huraira na ganin haka ta dage iface-iface kamar sabuwar kamu tana kiran Malam kawo mun ɗauki idanu na magana "

 

Tana cikin kukan ne ta hango wasu jajayen abubuwa na tunkaro inda take , su kuma idanuwan sai ƙara kumbura suke suna ƙara girma da yawa .

 

 

"Wayyo Malam kazo kai masu addu'ar da kace ta Aljanu ce dan Allah "

 

 

Tana cikin wannan lhun jan abin da take hangowa suka iso gabanta .

 

Ashe wasu gungun halittu ne su ba mata ba su ba maza ba, gashinsu har kan cibiyar su amma jajir yake sannan basu da Idanuwa ko alamar gun ƙwarin idanun babu a fuskarsu , gasu tamkar kalai barkono haka jikinsu yake jajir ba alamar fari ko baƙi tare dasu komi nasu jane .

 

 

Suna zuwa suka zagaye gun kamar su kaɗai ne agun birjik.

 

Kowa ne daga cikinsu yana riƙe da hannun ɗan uwansa na kusa dashi yana zuƙar jini , sai wani kalan nishi suke mai ban tsoro da razana zuciya .

 

Ai Huraira sai ta kwartsa ihu ta zabura ta dubi gabas da karfi ta fara jero addu'ar da rabonta da ita tun yarinta.

 

 

"Bisimillah zugum-zugum

Ina kuke mala'ikun zugum-zugum, ku bayyana ku mai da Aljanun nan zugum-zugum har in kai gidana suna zugum-zugum"

 

Ta dage iyakar karfinta tana maimaita addu'ar tsakaninta da Allah ita nan ne man tsari take daga waɗannan gungun mayun aljanun da suka sato ta daga kan gadonta zuwa lardin su na junnu .

 

Sai da ta jima tana addu'ar sannan ta buɗe idanunta, ganin wajen tayi fayau ba kowa hatta kattin idanuwa sun ruga sun bace suna gudun Mala'ikun zugum-zugum su zo  suna gun.

 

Murmushin tayi tace " ikon Allah wannan shi ake kira da magani a gonar yaro bai sani ba , to ai kuwa kun gama shan ruwa gabana tunda nagano lagon k.......

Bata gama ba taji kamar ana tafiya da ita saman sararin samaniya.

 

Cikin sauri ta kalli ƙasanta kaɗan ya hana lumfashinta ɗauke wa .

 

Ashe wanda yafi kowa tsayi da girma cikin halittun ya ɗauke ta ya kai saitin kunnensa domin a tunaninsa waƙace take sanda take kiran zugum-zugum ɗin.

Batai wata-wata ba taci gaba dakaranto addu'ar iyakar karfinta .

 

Sai da tayi harta gaji sannan ta buɗe idanunta ta sauke su kan halittun , yanzu kuma sai ɗaukar idanuwan suke suna kasawa a fuskarsu, ihu ta saki da karfi ta sume a hannunsa, hakan yayi dai-dai da bayyanar wata halitta tai masu wani yare nan da nan aka ɗauki Huraira dake sume aka nufi gidansu da ita basu ajeta ko inaba sai cikin kewayen gidan.

 

Malam da takaicin Huraira ya kamashi sosai yasashi ɗaukar buta ya nufi kewaye dan ya kama ruwa yayi alwala .

 

Ganin ta yayi kwance can gefen banɗakin ta shinfiɗa hijabinta (Abaya)dan tsabar munafinci ashe ta dawo gidan ganin ya riga ta dawowa yasata ɓoye banɗakin to Allah ya toni asirin ta yau dai .

 

Cikin fusatar abin da tai masa yasa ya ɗaga butar ya tsiyaya mata ruwan saitin fuskarta .

 

Firgigit ! Ta farka bakinta ɗauke da sunan Malam !

 

Hakan yasa ya ƙara aminta cewa abin da ransa ya raya masa haka ne ta aikata .

 

Ita kuma Huraira ganin ta kewaye tare da Malam yasata zabura da rugawa ɗakinta ta maido kofa ta rufe ko kula da ƙaramar ɗiyarta dake ɗauke da ledar da Nasir yaba da ana Bilkisu batai ba.

 

Malam ya jima yana godema Allah da ya tona asirin Huraira yau dai yasan gaskiyar yawace-yawacen da take fita idan bai nan .

 

Bilkisu na zaune ta gama sallah tana karatun Alkur'ani mai girma sai ga kanwarta ɗauke da ledar da Nasir ne kawai ke kawota gidan.

Shafawa tayi ta amshi ledar ta buɗe sai ga wata guntuwar takarda ta faɗo ƙasa daga cikin wani kwalin waya mai kyan gaske.

Buɗe kwalin wayar tayi aikuwa tasamu wata wata mai kyau sabuwa dal a ciki tare da gidan Sim ciki, takardar ta fara karantawa a bayyane.

"Amincin Allah ya tabbata gareki yake natsatsiyar zuciyata , ga waya nan ki buɗe ta an mata komi ga Number ta a ciki ki kirani Please dan insamu natsuwar aikin da nake yi .

 

 _Naki Nasir_

 

Batasan lokacin da murmushin ya suɓuce mata, ta kwashi kayan ta nufi gun Babansu dan ta gwada masa.

 

Lokacin zai shiga ɗakin Huraira yaji inda taje da munafinci da ya kaita kewaye har barci ya kwasheta ciki rabon asirinta ya tonu.

 

Dan haka ko wayar bai ansaba yayi dai addu'ar Allah yayi albarka yayi ɗakin Huraira abinsa.

 

Itakam Bilkisu da gudu ta koma ɗaki ta kunna wayar tayi dailing number Nasir dake ciki .

 

Bugu guda ta shiga cikin wayarsa .

Lokacin yana cikin kaiwa da komowa na tunanin Bilkisun shi sai ga kiranta , cikin farin ciki ya ɗaya kiran yana ambatar sunanta .

 

 

To koya su Inna da Malam zasu ƙare ?

Shi dai Malam ga tunaninsa .

Ita kuma Huraira ga abin da yasameta .

 

 Taku ce Haupha!!